Yanzu -Yanzu: Wani 'dan takarar ciyaman na jam'iyyar APC na kasa ya janye
Kwanaki uku kafin ranar da za'a yi taron gangamin jam'iyyar APC, dan takarar ciyaman, kuma tsohon gwamnan Jihar Edo, Osereimhen Osunbor ya janye daga takarar.
Mista Osunbor ya bayyana janyewarsa ne a wata sako da ya aike wa Premium Times inda ya ce ya yi hakan ne saboda girmamawa da ya ke yiwa shugaba Muhammadu Buhari.
A cikin sakonsa, ya kuma goyi bayan wani tsohon gwamnan jihar Edo, kwamared Adams Oshiomole a matsayin ciyaman na jam'iyyar APC na kasa.
KU KARANTA: Sanatan Najeriya ya fadi wuri biyu da ya kamata sojoji su nemi mayakan Boko Haram
Mr Osunbor ne dan takara na biyu da ya janye daga zaben kuma ya mara wa Adams Oshiomole baya wanda ya samu goyon bayan jiga-jigan jam'iyyar da shugaba Muhammadu Buhari.
Dan takarar da ya fara janyewa da farko shine Ibrahim Emokpaire, dan jam'iyyar APC mazaunin kasar Amurka.
Ya ce ya cinma wannan matsayar ne bayan ya yi shawara da iyalansa, abokansa da wasu yan jam'iyyar.
A sakonsa, Mr. Osunbor ya ce ya janye ne saboda baya son a tsawaita gudanar da zaben kuma saboda cigaban jam'iyyar baki daya.
"Na janye daga takarar zaben kuma na mara wa Adams Oshiomole baya," inji shi.
Ya bawa magoya bayansa hakuri musamman wanda basu so ya janye ba.
A halin yanzu, dan takara guda daya, Clement Ebri daga jihar Cross Rivers ne kawai zai kara da Adams Oshiomole.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng