Zaben Ekiti: Shekaru 4 da suka shude na masu kama karya ne, ranar 14 ga watan Yuli kuma na 'yanci ne - Oshiomole

Zaben Ekiti: Shekaru 4 da suka shude na masu kama karya ne, ranar 14 ga watan Yuli kuma na 'yanci ne - Oshiomole

Tsohon gwamnan Jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomole ya ce shekaru hudu da suka shude na masu kama karya ne amma ranar 14 ga watan Yuli na masu 'yanci ne.

Tsohon gwamnan ya fadi hakan ne a jawabin da ya yi a ranar Talata wajen yakin neman zaben Kayode Fayemi, dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar APC a Jihar Ekiti.

Ya yi kira ga al'ummar Jihar Ekiti su fito kwansu da kwarkwata suyi zabe saboda an kawar bata garin da ke tayar da zaune a jihar.

Zaben Ekiti: Shekaru 4 da suka shude na masu kama karya ne, ranar 14 ga watan Yuli kuma na 'yanci ne - Oshiomole
Zaben Ekiti: Shekaru 4 da suka shude na masu kama karya ne, ranar 14 ga watan Yuli kuma na 'yanci ne - Oshiomole

"Kar kuji tsoro, anyi maganin wadanda ke hadasa fitina a Jihar. Ku fito ku jefa kuri'ar ku a ranar 14 ga watan Yuli. Za ku samu kariya," inji shi.

KU KARANTA: Assha: 'Yan bindiga sun sace wani babban ma'aikacin NNPC

"Wani labari mai dadi kuma shine a ranar 14 ga watan Yuli, Fayemi ne dan takarar da za ku zaba. Alheri zata wanzu a jihar Ekiti. Shekaru hudu da suka shude na masu kama karya ne amma ranar 14 ga watan Yuli na masu 'yanci ne."

A jawabinsa, shugaban jam'iyyar APC na kasa Ahmed Bola Tinubu ya ce lokaci ya yi da ya kamata a samu canji a Jihar Ekiti. Ya ce Ekiti za ta shiga sahun jihohi masu cigaba.

"Ba za mu mayar da Ekiti baya ba. Ya zama dole ku fito kwanku da kwartkwata ku zabi jam'iyyar ACP," inji shi.

"Katin zabenku shine makamin ku. Kuyi amfani dashi wajen fatattakar PDP a ranar 14 ga watan Yuli."

Wani tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP da ya sauya sheka zuwa APC, Dayo Adeyeye ya ce jam'iyyar PDP ta mutu a Jihar.

"PDP ta mutu a Jihar Ekiti tun ranar 29 ga watan Mayu. Na fice daga jam'iyyar PDP kuma sauran mutane da dama za su biyo ni su dawo APC," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel