2019: Wani dan takarar shugaban kasa da ba Buhari ba, ya tara jama'a a Kano

2019: Wani dan takarar shugaban kasa da ba Buhari ba, ya tara jama'a a Kano

- Kungiyoyi irin su Kingsley Moghalu Support Organisation(KIMSO) da To Build A Nation (TBAN) na jihar sun karbe shi tare da sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi II da hannu biyu a fadar sarkin

- Kingsley Moghalu yayi alkawarin hannayen jari da kirkire kirkire na tattalin arziki wanda ba zai dogara da yare, addini ko matsayi ba

- Dan takarar shugabancin kasar yayi alkawarin farfado da masana'antu ta hanyar tallafawa bangarori da dama don samar da aiyukan yi, fadada tattalin arziki da kuma cigaba a kasar

2019: Wani dan takarar shugaban kasa da ba Buhari ba, ya tara jama'a a Kano
2019: Wani dan takarar shugaban kasa da ba Buhari ba, ya tara jama'a a Kano

A ranar Alhamis ne, 14 ga watan yuni, 2018,mazauna birnin kano suka fito kwai da kwarkwata don tarar Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Young Progressive Party, farfesa Kingsley Moghalu a zagayen kasa da yake yi.

Kungiyoyi irin su Kingsley Moghalu Support Organisation(KIMSO) da To Build A Nation (TBAN) na jihar sun karbe shi tare da sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi II da hannu biyu a fadar sarkin.

Kingsley Moghalu yayi alkawarin hannayen jari da kirkire kirkire na tattalin arziki wanda ba zai dogara da yare, addini ko matsayi ba.

Dan takarar shugabancin kasar yayi alkawarin farfado da masana'antu ta hanyar tallafawa bangarori da dama don samar da aiyukan yi, fadada tattalin arziki da kuma cigaba a kasar.

A maida martanin Sarkin Kano, yayi ma farfesan da mukarraban shi barka da zuwa tare da tuno nasarorin da Dan takarar ya samu a lokacin da yake babban bankin Najeriya.

DUBA WANNAN: Budaddiyar Wasika zuwa ga Hamza Al-Mustapha kan 2019

Kingsley Moghalu yayi alkawarin jari ga matan da aka horar karkashin Kingsley Women Skills Training, yace Gwamnatin shi zatayi yaki da talauci ta hanyar samar da kudi da ilimi ga mata da yara mata a kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel