12 Yuni: Babban dan Abilola ya tonawa Jonathan asiri, ya kwance masa zani a kasuwa
Babban dan marigayi Abiola, Kola Abiola, ya ce ba zai taba manta yadda tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi kememe a kan batun karrama mahaifin sa duk das au uku (3) yana rokon shi.
A satin da ya wuce negwamnatin Buhari ta karrama marigayi Abiola da lambar girma ta GCFR da kuma mayar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokraddiya ta Najeriya. Abiola ne ya lashe zaben shekarar 1993 amma gwamnatin soji ta Ibrahin Badamasi Babangida (IBB) ta hana shi hawa mulkin.
Da yake Magana a wani shirin gidan talabijin din Channels a jiya, Alhamis, Kola, ya ce ya nemi tsohon shugaban kasa Jonathan ya karrama mahaifin sad a lamabar GCFR amma saboda wasu dalilai na siyasa.
DUBA WANNAN: Goron Sallar shugaba Buhari ga Musulmin Najeriya
Kola y ace ya mika takardar bukatar hakan ga Jonathan ta hannun ministan shari’a na wancan lokacin, Mohammed Bello Adoke, a shekarar 2014 amma ya yi watsi da bukatar hakan.
Sannan ya kara da cewa ya kara nema a karo na biyu ta hannun Fasto Tunde Bakare gabanin zaben shekarar 2015 amma duk da bai amsa bukatar ba, Kola, y ace saida ya kara tuntubar Jonathan a kan bukatar bayan ya fadi zaben 2015 kafin ya mika mulki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng