Inda ran ka: Duba hotunan irin kayan tarihi da aka samu a tumbin wata shu’umar Akuya

Inda ran ka: Duba hotunan irin kayan tarihi da aka samu a tumbin wata shu’umar Akuya

Abun mamaki bay a karewa a Duniyar nan tamu, hakan ya saka Bahaushe ke cewa “inda ran ka, ka sha kallo”.

Kowa dai ya yarda cewar abincin da Akuya ta fi so ita ce ciyawa ko dusa ko kuma wasu nau’in abinci da mutane ke ci.

Amma sai ga shi an samu wata Akuya a Ajere dake jihar Kuros Riba na cin karfe tamkar wata jimina. Bayan yanka Akuyar an samu tarkacen karafa a cikin tumbin tad a suka hada da zobuna, kudaden karfe irin na duniyar da, agoguna da ragowar wasu tarkace.

Inda ran ka: Duba hotunan irin kayan tarihi da aka samu a tumbin wata shu’umar Akuya
Inda ran ka: Duba hotunan irin kayan tarihi da aka samu a tumbin wata shu’umar Akuya

Da yawan mutane ma basu kula da irin abubuwan da Akuyar ke ci ba sai bayan an yanka ta. Jama’a sun yi matukar mamakin irin abubuwan da suka gani hart a kai ga wasu na nuna shakkun cin naman Akuyar, su na masu bayyana cewar cin naman kan iya yiwa jikin mutum wani lahani.

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar, Hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) ta bayar da sanarwar mutuwar mataimakin shugabanta na kasa mai kula iyakoki, DCG Raymond Tonye Akra Jaja.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa nake farinciki da binciken da EFCC ke yi min – Babachir David Lawal

A wani jawabi da kakakin hukumar, Sunday James, ya fitar a jiya, Alhamis, hukumar ta bayyana cewar DCG Jaja ya mutu ne ranar 9 ga watan Yuni da muke ciki bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

Shugaban hukumar NIS na kasa, Muhammad Babanded, ya bayya a marigayin a matsayin mutum maid da’a da hukumar zata dade bata manta da shi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel