Shehu Sani Bai Ji Daɗin ba Seyi Tinubu Sarauta ba, Ya Faɗi Illar Hakan
- Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya shawarci sarakunan gargajiya su guji bai wa masu rike da mukaman gwamnati sarautu
- Gargadin nasa na zuwa ne bayan Sarkin Gwandu ya nada Seyi Tinubu, dan Shugaba Bola Tinubu, sarautar Dan Zakin Gwandu a jihar Kebbi
- A nasa bangaren, Shugaba Tinubu ya taya dansa murna, yana mai cewa sarautar na zuwa da nauyin da ya kamata ya sauke cikin kankan da kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi magana kan yadda sarakunan gargajiya ke bai wa masu rike da mukaman gwamnati da iyalansu sarautun gargajiya.
Shehu Sani ya bukaci sarakunan gargajiya da su guji irin wannan dabi’a, yana mai cewa bai kamata a rika karrama jami’an gwamnati da iyalansu da sarautu ba har sai sun kammala wa’adin aikinsu.

Kara karanta wannan
Gwamna ya jero dalilai 4 da suka sa zai yaƙi Tinubu a 2027 duk da ya goyi bayansa a 2023

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook bayan Sarkin Gwandu, Muhammadu Bashar, ya nada Seyi Tinubu sarautar Dan Zakin Gwandu a ranar Laraba a jihar Kebbi.
Shehu Sani ya bayyana ra'ayinsa kan sarautun gargajiya
Tsohon sanatan ya bayyana cewa bai wa mutanen da ke kan madafun iko sarautun gargajiya na iya rage martabar sarautun da kuma muhimmancin cancantar wadanda ake karramawa.
Shehu Sani ya ce:
"Mutanen da ke cikin gwamnati da 'yan uwansu bai kamata a ba su sarautun gargajiya ba har sai sun bar mukamansu. Daga nan ne za a iya karrama su da sarauta saboda hidimar da suka yi. Wannan shi ne ra'ayina."
An nada Seyi Tinubu sarautar Dan Zakin Gwandu, wadda ke nufin 'Dan Zakin Gwandu', a wani bikin da aka gudanar a fadar Abdullahi Fodiyo da ke Birnin Kebbi.
A cewar rahoton, Sarkin Gwandu ya ce an karrama Seyi ne saboda ayyukan taimakon al'umma da yake gudanarwa, da kuma gudummawar da yake bayarwa wajen bunkasa rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan
Mataimakin shugaban majalisa ya ga ta kansa da ya yi ƙokarin tallata Tinubu a taron jama'a

Source: Facebook
Tinubu ya taya Seyi murna
A wani bangare kuma, Shugaba Bola Tinubu ya taya dansa murnar samun wannan sarauta, yana mai godiya ga Sarkin Gwandu da majalisar masarautar bisa karramawar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana cewa wannan karramawa ta farko ce irinta a tarihin masarautar.
Shugaban kasar ya ce sarautar ba wai karramawa ce kawai ga dansa ba, har ma tana zuwa da nauyin da ya shafi jagoranci, hadin kai da yi wa al'umma hidima.
Tinubu ya ce a matsayinsa na uba, yana farin cikin ganin wata masarauta mai dadadden tarihi ta karrama dansa.
An ba yar sarauta a Katsina
A baya, an ji cewa Sarkin Daura ya karrama Folashade Tinubu-Ojo, ’yar Shugaba Tinubu, saboda gudunmawarta wajen ci gaban al’umma da mata baki daya.
Sarkin Daura ya kuma nada Minista Hannatu Musa Musawa sarautar Mairamar Kasar Hausa, yayin bikin Hawan Magajiya da aka gudanar a fadar masarautar.
Bikin ya samu halartar Gwamna Dikko Umaru Radda da manyan jami’an gwamnati, sarakuna da masu rike da sarautun gargajiya daban-daban daga sassa daban-daban.
Asali: Legit.ng