Sadaukarwar ku ba zata tafi a banza ba – Shugaba Buhari ya bawa ‘yan Najeriya karfin gwuiwa a sakon barka da Sallah

Sadaukarwar ku ba zata tafi a banza ba – Shugaba Buhari ya bawa ‘yan Najeriya karfin gwuiwa a sakon barka da Sallah

Shugaba Buhari ya yi kira ga musulmi da su dore da halayen kirki har bayan azumin watan Ramadana mai alfarma.

Bayan hakan, ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su raba addini da tarbiya, domin a cewar sa, yin hakan zai bayar da kafa ga balagurbin shugabanni.

A cikin sakon nasa, ga musulmi, na kammala azumi, shugaba Buhari ya yiwa musulmi murnar ganin watan Ramadana tare da bukatar su zama masu koyi da kyawawan halayen masu azumi domin zama wakilan Musulunci na kwarai.

Sadaukarwar ku ba zata tafi a banza ba – Shugaba Buhari ya bawa ‘yan Najeriya karfin gwuiwa a sakon barka da Sallah
Shugaba Buhari

Kazalika, shugaba Buhari ya nuna takaicin sa bisa yadda son kai da hadama suka yi katutu a zukatun mu hart a kai ga wasu na mancewa da tarbiyya saboda hakan.

Shugaba Buhari ya nuna mamakin wanda zai ce yana da imani amma ya zamana yin mugunta ga wasu shine sana’ar sa ko kuma hanyar samun ribar kasuwanci.

DUBA WANNAN: Bayan daure 'yan APC; Nyame da Dariye, EFCC ta ambaci wani tsohon da zata mayar da hankali kan sa

Sannan ya kara yin kira ga gama-garin ‘yan Najeriya da su daina girmama barayi domin ba masu gina rayuwar al’umma ba ne saidai rusa ta.

Bayan ya bukaci malamai da su cigaba da yiwa kasa addu’ar zaman lafiya, shugaba Buhari ya godewa ‘yan Najeriya bisa hakurin su tare da basu tabbacin cewar, sadaukarwar sub a zata tafi a banza ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel