A yau kotu zata kara yankewa wani tsohon gwamnan PDP hukunci

A yau kotu zata kara yankewa wani tsohon gwamnan PDP hukunci

A yau ne wata babbar kotun Abuja zata yanke hukunci a kan shari’ar tsohon gwamnan jam’iyyar PDP, Joshua Dariye, a jihar Filato da aka gurfanar da laifin almundahana da kudin jama’a lokacin da yake gwamna.

Ana tuhumar Dariye da laifin karkatar da biliyan N1.162 daga asusun jihar Filato lokacin zangon mulkin sa daga shekarar 1999 zuwa 2006.

An fara zaben Dariye a matsayin gwamnan jihar Filato a shekarar 1999 kafin daga bisani a sake zabar sa a karo na biyu a shekarar 2003, saidai an tsige shi a shekarar 2006 kafin daga bisani kotu tayi umarnin a mayar das hi ya karasa zangon mulkin sa a shekarar 2007.

A yau kotu zata kara yankewa wani tsohon gwamnan PDP hukunci
Joshua Dariye

Bayan kamala zangon mulkin san a biyu ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar das hi gaban kotu a watan Mayun 2007 a kan wasu laifuka 21 da suka hada da wawure kudi tare da fitar da su kasashen ketare ta hanyar amfani da ofishin san a gwamna.

Duk kokarin Dariye na ganin hukumar EFCC bata cigaba da tuhumar sa bay a ci tura bayan wata kotun tarayya ta soke hukuncin wata kotu da ta dakatar da sauraron karar na tsawon shekaru 7 tare da umarnin cigaba da tuhumar sa a shekarar 2015.

DUBA WANNAN: Tsohon gwamna Oshimhole ya bayyana abinda zai yi idan ba a zabe shi shugaban jam'iyyar APC ba

Yanzu haka Dariye Sanata ne a jam’iyyar APC duk da kasancewar an zabe shi ne a karkashin tutar jam’iyyar PDP da ya yi gwamna a cikin ta.

Olasumbo Banjoko, alkaliyar da ta yankewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame, hukunci c eta saka yau, Talata, a matsayin ranar da zata yanke hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel