Sauki ya fara samuwa: Soji sun halaka 'yan bindiga 11 a Kaduna

Sauki ya fara samuwa: Soji sun halaka 'yan bindiga 11 a Kaduna

Dakarun soji daga 1 Division a Kaduna sunyi nasarar halaka wasu yan bindiga 11 a ranar Alhamis yayin da suka kai simame a kasuwanin wasu kauyuka a jihar.

A sanarwan da ya fitar ranar Asabar, kakakin hukumar, Brig. Janar Texas Chukwu ya ce anyi simamen ne a kauyukan Kidandan, Maidaro da Sabon Fili inda yan bindigan ke hallartan kasuwanin kauye don siyan kayayakin da suke bukata.

Sauki ya fara samuwa: Soji sun halaka 'yan bindiga 11 a Kaduna
Sauki ya fara samuwa: Soji sun halaka 'yan bindiga 11 a Kaduna

A cewarsa, bayan an tsegunta wa hukumar sojin, dakarun sojin da kuma yan banga sun shiga kasuwan inda suka bar da kama don su gano yan bindigan.

KU KARANTA: An damke wata mahaifiya da ta kashe jaririn ta a Sakkwato

"Jim kadan bayan sojojin da sauran jami'an tsaron sunyi ido biyu da yan bindigan, anyi musayar wuta zazafa tsakanin jami'an tsaron da yan bindigan da ke kokarin tserewa.

"Sai dai dakatun sojojin mu sun ci galaba a kan yan bindigan inda suka kashe 12 daga cikinsu yayin da suke kokarin tserewa," inji Chukwu.

Ya kuma ce sojin sun kwato babur 32, wayoyin salula biyar da kudin N9,135.

A wata rahoton, Legit.ng ta ruwaito muku inda dakarun sojin Najeriya suka harbe yan baranda biyar yayin wani simame da suka kai yankunan da ta'addanci ya yi kamari a karamar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Dakarun sojin masu atisayen Idon Raini ne suka kai simamen cikin kauyukan Danguru da Babandoka da Dansadau duk a karamar hukumar Maru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel