Shugaba Buhari ya sake yin babban nadi mai muhimmanci a CBN
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Folashodun Adebisi Shonubi a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
Za'a rantsar da shi ne bayan majalisar dattawa ta amince da nadin.
Hadimin shugaban kasa a fanin yadda labarai, Garba Shehu ne ya bayar da wannan sanarwan a ranar Juma'a.
A yanzu, Folashodun Shonubi ne babban direktan Hukumar sulhunta bankuna da biyan kudade a turance Nigeria Inter-Bank Settlement Plc (NIBSS).
NIBSS tana daya daga cikin hukumomin da gwamnatin tarayya ke amfani dashi wajen biyan kudade da albashin ma'aikata a hukumomi daban-daban a Najeriya.
KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta yi kira ga shugaba Buhari ya karrama Kudirat Abiola
Kafin ya zama shugaban NIBSS a shekarar 2012, Shonubi ya yi aiki na shekaru masu yawa a fannin harkokin kudi daya daga cikinsu shine Babban Direkta a Union Bank Plc, ya kuma shugabanci Renaissance Securities Nigeria Limited da kuma Eco Bank Plc.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng