Soja mazan fama: Wani jarumin soja ya kwace bindiga daga hannun 'dan fashi da makami

Soja mazan fama: Wani jarumin soja ya kwace bindiga daga hannun 'dan fashi da makami

- Wani soja ya nuna jarumtaka da bajinta yayin da yayin da 'yan fashi suka tare motar fasinjoji da ya ke ciki

- Sojan ya yi kokowa kuma ya ci galabar dan fashin inda ya kwace bindigar kirar AK 47 da ke hannunsa

- Jarumin sojan ya sami rauni sakamakon arangamar amma yanzu yana samun sauki a asibiti

Soja mazan fama: Wani jarumin soja ya kwace bindiga daga hannun dan fashi da makami
Soja mazan fama: Wani jarumin soja ya kwace bindiga daga hannun dan fashi da makami

Wani jarumin soja da ke bataliyar 120 Gonori a jihar Yobe ya yi bajinta inda ya kwace bindiga kirar AK 47 daga hannun wani dan fashi da makami a titin Lafia zuwa Makurdi a garin Daudu da ke karamar hukumar Gunman na jihar Benue.

KU KARANTA: An gano kwayar da tafi haukata matasa a jihar Kano

Kakakin hukumar sojojin Najeriya, Mista Texas Chukwu ne ya tabbatar da afkuwar lamarin a wata sanarwa da ya bayar a yau Alhamis a babban birnin tarayya Abuja.

Mr Chukwu ya ce lamarin ya faru ne a jiya yayin da wasu gungun yan fashi suka tare motar da sojan ke ciki.

Sai dai ya ce jarumin sojan ya samu rauni a yayin da suke kokowa da dan fashin amma ya yi nasarar kwace bindigar AK 47 din tare da harsashi na musamman guda biyar da ke tare dashi.

"A halin yanzu sojan yana asibiti inda ake kulawa da lafiyarsa," inji Mista Chukwu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel