Saraki ya sha ruwa tare da su Ali Nuhu, kalli hotuna

Saraki ya sha ruwa tare da su Ali Nuhu, kalli hotuna

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya karbi bakuncin wasu jarumai da masu shirya fina-finan Kannywood a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Tawagar Kannyood din sun kai ziyara gidan shugaban majalisar ne karkashin jagorancin fitaccen jarumi Ali Nuhu da Saliyu Aliyu da Tijjani Faraga da kuma Maryam Habila.

Mai dakin shugaban majalisar Misis Tosin Saraki ta taya maigidanta tarbar bakin a gidansu har ma ta wallafa a shafinta na sada zumunta na Instagram cewa tayi farin cikin taya mijinta tarbar tawagar 'yan Kannywood a gidansu don yin bude baki a jiya.

Misis Saraki kuma ta mika godiyarta kan gayyatar da 'yan wasan hausa mata su kayi mata zuwa wajen da ake daukar fim inda ta kara da cewa Insha Allahu za ta hallarci wajen ko dan ta kara goge wa a yaran Hausa.

Saraki ya sha ruwa tare da su Ali Nuhu
Saraki ya sha ruwa tare da su Ali Nuhu

Saraki ya sha ruwa tare da su Ali Nuhu
Saraki ya sha ruwa tare da su Ali Nuhu

KU KARANTA: Dalilin da yasa na watsa wa mahaifin yara na tafasashen ruwa - Wata mata

Saraki ya sha ruwa tare da su Ali Nuhu
Saraki ya sha ruwa tare da su Ali Nuhu

Saraki ya sha ruwa tare da su Ali Nuhu
Saraki ya sha ruwa tare da su Ali Nuhu

Saraki ya sha ruwa tare da su Ali Nuhu
Saraki ya sha ruwa tare da su Ali Nuhu

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164