Zan sake tsayawa takarar gwamna - Mama Taraba

Zan sake tsayawa takarar gwamna - Mama Taraba

Ministar harkokin mata ta Najeriya, Sanata Aisha Alhassan ta sake bayyana aniyarta ta sake tsayawa takarar gwamnan jihar Taraba a zabe mai gabatowa na shekarar 2019

Zan sake tsayawa takarar gwamna - Mama Taraba
Zan sake tsayawa takarar gwamna - Mama Taraba

Ministar harkokin mata ta Najeriya, Sanata Aisha Alhassan ta sake bayyana aniyarta ta sake tsayawa takarar gwamnan jihar Taraba a zabe mai gabatowa na shekarar 2019.

"Kowa yasan da sanin cewa nice na lashe zaben gwamnan jihar nan a shekarar 2015, har babbar jam'iyyar adawa ma ta PDP ta shaida cewar nice na lashe zaben, saboda haka zan sake tsayawa takara a zabe mai zuwa inda har Allah yasa ina raye.

DUBA WANNAN: Zargin aikata zina a watan Ramadan yasa sunyi mata dukan kawo wuka

"Na san da cewa komai iko ne na Allah, na san Allah ne bai nufe ni da zama gwamnan jihar nan ba. Na lashe zaben 2015, amma Allah bai so na hau kujerar gwamnan ba. Zan cigaba da yarda da nufin Allah da kuma cigaba da zama tare da mutanen jihar Taraba, kuma na san idan har Allah yaso zan lashe zaben 2019," inji ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng