Biafra: Najeriya ta tafka asarar biliyan 250 a makon nan kadai
- Anyi kira ga kabilar Ibo a kudancin Najeriya da su zauna a gida a Mayu 30
- Sunyi zamansu a gida sunki zuwa aiki a makon jiya
- An tafka asara saboda hada-hadar da suka ki yi ta kudi
Naira biliyan kusan 250 ne gwamnati da 'yan Najeriya su yi asara bayan da kabilar Ibo taki yin aiki a ranar 30 ga watan Mayu da ya gabata domin tunawa da kasar da suka taba kafawa ta Bayafara a shekarun 1960s.
Kasar ta Bayafara dai ta rushe a 1960 bayan watanni 30 da aka kafa ta wanda ya jawo yakin basasa.
A makon nan ne dai aka yi kira ga 'yan kabilar da su zauna gida kar suyi aiki ko kasuwanci a wannan rana don nuna goyon baya da kafa kasar a nan gaba.
DUBA WANNAN: Ashe an jima Yarima Salman ciwo ne yayin kokarin juyin mulki
Kungiyoyin dake dabbaka wannan aniya sun hada da IPOB da MASSOB. Suna barazanar fada ga gwamnati ta tarayya kuma suna yawan barazana ga jama'ar su da suka ki yi musu biyayya a yankin na kudancin kasar nan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng