Sojojin Najeriya sun kama Tireloli makare da alburusai 300,000 da ta nufo Najeriya

Sojojin Najeriya sun kama Tireloli makare da alburusai 300,000 da ta nufo Najeriya

Jami’an hukumomin tsaron Najeiriya da suka hada da jami’an Soji, Yansanda da na hukumar DSS sun samu nasarar dakile shigo da wasu dimbin alburusai zuwa Najeriya, kamar yadda rahoton jaridar Rariya ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Mayu, inda jami’an tsaro suka yi ram da wasu Tireloli dake dauke da alburusai fiye guda dubu dari uku, 300,000, sun nufo Najeriya akan iyakar kasar Bini da Najeriya.

KU KARANTA: Tsugunni bata kare ba: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane 25 a jihar Kaduna

Sai dai majiyar ta bayyana cewa direbobin motocin, da sauran masu kokarin shigo da alburusan gida Najeriya sun ranta ana kare, ma’ana jami’an tsaron basu samu nasarar cafke ko daya daga cikinsu ba.

Sojojin Najeriya sun kama Tireloli makare da alburusai 300,000 da ta nufo Najeriya
Alburusai

A wani labarin kuma, Dakarun Sojin Najeriya dake aikin kakkabe ragowar yan ta’addan Boko Haram dake yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun samu nasarar halla yan ta’adda guda uku tare da ceto mutane tara.

Bugu da kari wasu Sojojin Najeriya guda biyar sun gamu da ajalinsu a wani harin kwantan bauna da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai musu a wani kauye dake karamar hukumar Gwoza, sai dai suma yan ta’addan sun yi asarar mayaka da dama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng