2019: Mashahurancin Shugaba Buhari shi zai tabbatar da Nasarar jam'iyyar APC - Umar Bago

2019: Mashahurancin Shugaba Buhari shi zai tabbatar da Nasarar jam'iyyar APC - Umar Bago

Wani dan majalisar wakilai na jihar Neja, Umar Bago, ya bayyana kyakkyawan zaton sa dangane da samun nasarar jam'iyyar APC wajen lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2019.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dan majalisar ya bayyana hasashen sa yayin ganawa da manema labarai a babban birnin jihar na Minna.

Honarabul Bago yake cewa, mashahurancin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasar nan shi zai tabbatar da nasarar sa a zaben 2019.

Bago ya shaidawa manema labarai cewa, har yanzu shugaba Buhari yana ribatar soyayyar al'ummar kasar da yake ci gaba da kasancewa dan siyasa mafi girman tasiri akan al'ummar Najeriya.

2019: Mashahurancin Shugaba Buhari shi zai tabbatar da Nasarar jam'iyyar APC - Umar Bago
2019: Mashahurancin Shugaba Buhari shi zai tabbatar da Nasarar jam'iyyar APC - Umar Bago

Ya ci gaba da cewa, Buhari shine zakaran gwajin dafi cikin 'yan siyasar kasar nan ta fuskar yawan mabiya da masoya.

KARANTA KUMA: Babu Alkawarin da na dauka yayin yakin neman Zabe a 2015 - Gwamna Bello

A kalaman sa, "shugaba Buhari yana da mabiya tamkar wadanda ya asirce musamman a cikin matasa da kuma mata daga addinai, kabilu, al'adu da ra'ayoyin siyasa daban-daban."

'Dan majalisar mai wakilcin mazabar Chanchaga a majlisar wakilai ya kuma shawarci shugaba Buhari akan mayar da hankali da bayar da kulawa wajen ci gaba da yakar cin hanci da rashawa, ta'addanci gami da tsageranci da kuma habakar tattalin arziki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng