Liverpool da Madrid: Allah ne ya hukunta Salah saboda kin yin azumi - Malamin Islama

Liverpool da Madrid: Allah ne ya hukunta Salah saboda kin yin azumi - Malamin Islama

- Wani mai wa'azin addinin musulunci, Mubarak Al-Bathali ya alakanta raunin da Mohammed Salah ya yi a ranar 26 ga watan Mayu da rashin yin azumi

- A ranar da aka buga wasar karshe na kofin kwararu tsakanin Real Madrid da Liverpool a garin Kiev ne sallah ya ajiye azuminsa na watan Ramadan

- Salah ya sami rauni a kashi na farko na wasan wanda Al-Bathi ya yi ikirarin cewa Allah ne ya hukunta shi saboda ajiye azuminsa a ranar

Wani mai wa'azin addinin musulunci dan kasar Kuwaiti, Mubarak Al-Bathali ya fadi karar cewa rashin yin azumi da dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohammed Salah ya yi a ranar 26 ga watan Mayu ne ya janyo masa fushin Allah a wasar karshe da suka buga a Kiev.

Liverpool da Madrid: allah ne ya hukunta Salah saboda kin yin azumu - Malamin Islama
Liverpool da Madrid: allah ne ya hukunta Salah saboda kin yin azumu - Malamin Islama

Mohammed Salah dai ya yi gwagwarmayar neman kwallo ne da mai taimakawa wajen tsaron gida na kungiyar Madrid, Sergio Ramos wanda hakan ta haifar masa jin rauni a kafadarsa kuma daga baya ya fice daga wasar bayan mintuna 30 da farawa saboda radadi.

KU KARANTA: Sharudda hudu da 'yan nPDP suka gindayawa jam'iyyar APC

Da farko dai, an ruwaito cewa Mohammed Sallah zai yi azumi a ranar wasan karshe ta cin gasar kwararu da za'ayi a birnin Kiev amma daga bisani sai likitan kungiyar Liverpool ya tabbatar da cewa ba zai yi azumi a ranar ba.

Ya dai ajiye azuminsa a ranar 26 ga watan Mayun 2018 amma bai samu ikon kammala karo na farko a wasar ba kuma daga baya kungiyarsa ta Liverpool tayi rashin nasara inda kungiyar Real Madrid ta doke Liverpool din da 3-1.

Sai dai malamin kasar Kuwaiti, Mubarak al-Bathali ya ce Salah ya yi zunubi saboda ajiye azumi da ya yi a dalilin kwallon inda ya kara da cewa bashi da kwakwaran dalili a addinance na ajiye azumin.

"Allah ne ya hukunta shi saboda ya ajiye azumi, kuma zai fuskanci hukuncin da zai biyo baya.

"Kada kayi tunanin cewa dabara da kokari ne ke tafiyar da rayuwar musulmi, rayuwa na hannun Allah ne kuma shi ya ke juya ta yadda ya so.

"Wata kila ma raunin da ka samu alkhairi ne gare ka," kamar yadda mai wa'azin kasar ta Kuwaiti ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164