Wani Lauyan Kasar waje ya soki Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari

Wani Lauyan Kasar waje ya soki Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari

- Wani Lauya yace kusan babu banbanci tsakanin Gwamnatin Buhari da mulkin Soji

- Emmanuel Ogebe yayi wani dogon jawabi a Ranar bikin Damukaradiyya na Kasar

- Babban Lauyan yace Shugaban Kasa Buhari bai san manufofin tsarin farar hula ba

Wani Lauya da ake ji da shi a Duniya mai rajin kare hakkin Bil-Adama mai suna Emmanuel Ogebe yayi kaca-kaca da Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari inda yace sam Shugaban kasar bai san tsarin Damukaradiyya ba.

Lauyan Kasar waje ya soki Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari
Lauya mai rajin kare hakkin Jama'a a kasar waje ya soki Buhari

Emmanuel Ogebe yayi jawabi ne a Ranar Damukaradiyya ta kasar a Legas inda ya zargi Shugaban kasar da kokarin ganin-bayan ‘Yan adawar sa na siyasa. Ogebe yace Shugaba Buhari ya saba tattake martabar Damukaradiyya a kasar.

KU KARANTA:

Babban Lauyan yayi tir da yadda ake yakar ta’addanci a Kasar inda yace akwai son zuciya da nuna banbancin addini wajen Shugaba Buhari. Lauyan ya kuma sa alamar tambaya kan ‘Yan Matan Chibok da Dapchi da aka sace a baya.

Sahara Reporters ta rahoto Emmanuel Ogebe yana cewa mulkin Shugaba Buhari yayi kama da kama-karyar mulkin Sojoji. Ogebe yace babu abin da Gwamnatin Buhari ta sa gaba sai karyar tsiya da kuma yaudarar Jama’ar kasar nan.

Shi dai wannan Lauya yana gani Shugaba Buhari ya ba ‘Yan Najeriya kunya har a waje inda babu abin da yake yi sai daura laifin lalacewar kasar nan wasu Shugabannin a baya da kuma surutun kama barayin Gwamnati dare-da-rana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel