Katin Zabe Da Na'urar sa ne suka taka rawar gani wajen nasara ta a Zaben 2015 - Buhari

Katin Zabe Da Na'urar sa ne suka taka rawar gani wajen nasara ta a Zaben 2015 - Buhari

Da sanadin shafin jaridar Vanguard mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana babban dalilin da ya sanya ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2015 da ta gabata.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa katin zabe tare da na'urar sa ne suka taka rawar gani wajen samun nasara a zaben na 2015.

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a daren ranar Talatar da gabata yayin jawaban sa na buda baki tare da wasu jiga-jigai na sashen shari'a dake kasar nan.

Katin Zabe Da Na'urar sa ne suka taka rawar gani wajen nasara ta a Zaben 2015 - Buhari
Katin Zabe Da Na'urar sa ne suka taka rawar gani wajen nasara ta a Zaben 2015 - Buhari

Shugaban yake cewa, ingantacciyar hanyar dakile magudi da katin zabe tare da na'urar sa suka haifar ya sanya yayi nasara a zaben 2015 bayan ya sha mugun kayi har karo uku a baya.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Osinbajo yayin ganawa da tawagar jam'iyyar nPDP

A sanadiyar haka ne shugaba Buhari yake kiran gwamnoni kasar nan dangane da fadakar da al'ummomin jihohin su akan mallakar katin zabe da sanin muhimmancin sa da zai kwato ma su 'yancin su.

Ya kara da cewa, wannan sabuwar hanyar fasahar zamani da katin zabe da na'urar sa ya kawo a kasar nan ya tsarkake dukkan wani nau'i gami da dakile magudin zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel