Tsofaffin 'Yan PDP da wasu manyan 'Yan siyasa na kus-kus din barin APC

Tsofaffin 'Yan PDP da wasu manyan 'Yan siyasa na kus-kus din barin APC

Kwanaki tsofaffin ‘Yan Jam’iyyar PDP da su ka narke cikin tafiyar APC su ka kai kukan su wajen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari inda su ka koka da cewa ba a tafiya da su a Gwamnatin nan. Yanzu haka dai su na neman barin APC.

Bayan takardar dai, Uwar Jam’iyyar ta zauna da Alhaji Kawu Baraje da sauran Manyan nan PDP. A sakamakom haka ne ‘Yan nPDP su ka shirya wani taro bayan nan domin fitar da matsaya inda da dama su ke tunanin barin Jam’iyyar.

Tsofaffin 'Yan PDP da wasu manyan 'Yan siyasa na kus-kus din barin APC
Jirgin da ya dauko Jam'iyyar APC yana cikin matsala

Wadanda su ka halarci taron nan sun hada da Shugabannin Majalisar Tarayya Bukola Saraki, da Yakubu Dogara, da kuma tsohon Shugaban MajalisaGwamna Aminu Waziri Tambuwal da irin su tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.

Wani ‘Dan Majalisa da ma ba ya cikin tafiyar nPDP da ya halarci taron yace ba su yanke shawarar Jam’iyyar da su koma ba idan su ka bar APC. ‘Dan Majalisar yace wulakancin da ake yi wa ‘Ya ‘yan Jam’iyyar irin su Dino Melaye yayi yawa.

Ragowar wadanda su ke wajen taron sun hada da Prince Oyinlola, Murtala Nyako, Adamu Aliero; Danjuma Goje; John Enoh; Andy Uba; Ibrahim Gobir; Rufai Ibrahim; Ibrahim Danbaba; Suleman Nazif; Isa Misau; Muhammed Shitu; Shehu Sani; Dino Melaye; Suleiman Hunkuyi.

KU KARANTA: Fadar Shugaban Kasa ta caccaki tsohon Shugaba Jonathan

Haka kuma akwai ragowar Sanatoci irin Shaaba Lafiagi; Bala Ibn Na’Allah; David Umaru; da Barnabas Gemade. Haka kuma akwai ‘Yan Majalisa irin su Aminu Shagari; Kabiru Marafa Achida; Isa M. Ashiru; Muh’d Musa Soba; Mark Gbillah; da Sani Mohammed Rano.

Sauran ‘Yan Majalisar da su halarci taron sun hada da Garba Umar Durbunde da Aliyu Madaki, da kuma irin su Zakari Mohammed, Rufai Ahmed Chachangi; Razak Atunwa; Emmanuel M. Udende; Hassan Saleh; Nasiru Garo Sule; Orker Jev; Aliyu Ahman Pategi; Isah Halilu.

Daily Trust tace haka kuma akwai su Rabiu Garba Kaugama; Abdussamad Dasuki; Ismaila A. Gadaka; Lado Suleja; Dickson Tarkighir; Babatunde Kolawole; B. Ayorinde; Danjuma Shida; Danburam Nuhu; Sunday Adepoju; Sani Zorro; Ahmed Garba Bichi; da Garba Ibrahim Mohammed.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: