Manyan ayyukan da Sanata Ali Wakili yayi wa Mazabar sa lokacin yana da rai

Manyan ayyukan da Sanata Ali Wakili yayi wa Mazabar sa lokacin yana da rai

Wannan karo mun tuna da Marigayi Ali Wakili wanda ya rasu kwatsam kwanaki yana wakiltar Kudancin Jihar Bauchi a Majalisar Dattawa kwanakin baya. Kafin Sanatan ya rasu yayi wa al’ummar sa ayyuka na cigaban kasa.

Manyan ayyukan da Sanata Ali Wakili yayi wa Mazabar sa lokacin yana da rai
Marigayi Sanata Ali Wakili lokacin yana Majalisar Dattawa

A lokacin rayuwar sa an rahoto cewa ‘Dan Majalisar wanda shi ne Shugaban Kwamitin jin dadi da walwalar al’umma yayi wa mutanen Bauchi ta Kudu ayyuka sama da 14 na a zo-a gani cikin shekaru kusan 3 da yayi a Majalisar.

Daga ciki akwai ayyukan samar da ruwa da sha’anin noma da kuma bangaren ilmi da kiwon lafiya da kuma bangaren ICT na zamani.

KU KARANTA: Tsohon 'Dan Majalisa zai yi takarar kujerar Sanatan Bauchi

  1. A bangaren samar da ruwa da kuma inganta noma, an haka rijiyoyin burtsatsi sama da 50 da kuma rijiyoyin ruwa a Kauyuka da dama.
  2. Sanatan ya kuma haka rijiyoyin ruwa na zamani sama da 100 domin inganta noman rani a Kauyukan da ake wahalar ruwa.
  3. Sanata Ali Wakili ya kuma ba manoman Yankin sa taki da irin zamani duk a Kudancin Jihar na Bauchi domin a samu amfanin noma.
  4. Haka kuma Mai dakin Sanatan ta sayawa maoma kayan noma ga ‘Yan uwan sa Mata domin rage talauci wajen Matan Gari.
  5. Sanatan yace ya kuma horas da ‘Yan mata sana’o’in da su ka hada da dinki da kitso da saka da sauran su domin su samu na hannun su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng