Gwamnatin shugaba Buhari za ta gina layin dogo da zai sada wasu jihohin Najeriya da Jamhuriyar Nijar

Gwamnatin shugaba Buhari za ta gina layin dogo da zai sada wasu jihohin Najeriya da Jamhuriyar Nijar

Domin inganta rayuwar al'umma da kasuwanci da mu'amala tsakanin juna, gwamnatin shugaba Buhari za ta gina layin dogo da zai faro daga garin Fatakwal ya ratsa wasu jihohin Najeriya kana ya dire a jamhuriyar Nijar.

Wannan ya biyo bayan amincewa da mayar da hankali a kan wasu muhimman abubuwa uku da majalisar zartarwa na Najeriya ta yi don inganta rayuwar mutanen kasar.

Gwamnatin shugaba Buhari za ta gina layin dogo da zai sada wasu jihohin Najeriya da Jamhuriyar Nijar
Gwamnatin shugaba Buhari za ta gina layin dogo da zai sada wasu jihohin Najeriya da Jamhuriyar Nijar

Wadannan muhimman abubuwa sune kiwon lafiya da sufuri da kuma al'amurran da suka shafi ciyar da kasar gaba da bulo da ababen more rayuwa ga al'umma kamar yadda muryar Amurka hausa ta ruwaito.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sha suka a kan yabon Abacha

Majalisar ta amince da cewa akwai bukatar gina layin dogo wanda zai taso daga garin Fatakwal ya kuma ratsa da Abuja da Kaduna da Kano da Maiduguri kana ya wuce har Jamhuriyar Nijar.

Wannan yana daya daga cikin ayyukan da gwamnatin kasar keyi don ganin ta bunkasa harkokin kasuwanci da cinikkayya da kuma inganta mu'amala tsakanin al'umomin jihohin Najeriya da ma kasar ta Nijar.

Bayan aikin gina layin dogon, majalisar har ila yau ta amince da daukan matakai a kan shigowa da suga cikin Najeriya. Bugu da kari, za'a inganta ayyukan jami'an kwastam na Najeriya domin su rika tattara bayanan a kan masu shige da fita daga kasar.

Ministan harkokin cikin gida, Janar Abdulrahman Dambazau (murabus) ya ce za'a gina wa hukumar kwastam din wani katafaren ofishi wanda zai kunshi dukkan kayayakin ayyuka da suke bukata don tattara bayanai a kan masu shige da fice a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164