Yadda mahaifina ya shafe tsawon shekaru 4 yana lalata da ni – Wata matashiya

Yadda mahaifina ya shafe tsawon shekaru 4 yana lalata da ni – Wata matashiya

Wata matashiyar budurwa mai shekaru 18 a duniya ta shaidawa wata kotu dake Ikeja a jihar Legas cewar, mahaifin ta, Folorunso Oluwaseuyn; mai shekaru 52, ya shafe tsawon shekaru hudu yana tilasta mata yin lalata da shi.

Matashiyar, da ba a bayyana sunan tab a, ta bayyana cewar mahaifin nata ya fara yi mata fyade tun tana da shekaru 12 lokacin da ta koma gidan sa dake unguwar Ikorodu a Legas da zama.

Yadda mahaifina ya shafe tsawon shekaru 4 yana lalata da ni – Wata matashiya
Yadda mahaifina ya shafe tsawon shekaru 4 yana lalata da ni – Wata matashiya

Da take bayar da shaida a gaban alkalin kotun, Sybil Nwaka, matashiyar tace, “ni da ragowar ‘yan uwana hudu muna zaune ne a daki daya a wani gidan haya. Watarana mahaifina ya kira ni tare da shaida min cewar nono nay a fi na ‘yar uwa ta girma, a saboda haka zai zuke min abinda ya fito a ciki. A wannan ranar ne ya fara tilasta min yin lalata da shi lokacin ina aji a makarantar sakandire.”

Matashiyar ta kara da cewar, ta shaidawa ‘yar uwa ta abinda ya faru amma babu abinda zata iya yi a kan hakan.

DUBA WANNAN: Abinda muka tattauna da shugabannin hukumomin tsaro - Saraki

Sannan ta cigaba da cewa, “haka ya cigaba da yin lalata da ni yana bani rowan gishiri da sukari. Duk kokarina na dakatar da shi bai yi aiki ba, sai yace min wai “ko Allah ya sani bashi da mata”, sannan kuma wai ba zai samu kudin da zai dauki nauyin dawainiyar mu ba idan bai kwanta da ni ba.”

Mai shari’a Nwaka ya daga sauraron karar ya zuwa ranar 21 ga watan Yuni, 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel