Rikicin APC babbar dama ce ga jam'iyyar PDP - Sanata Gyunka

Rikicin APC babbar dama ce ga jam'iyyar PDP - Sanata Gyunka

Wani Sanata da yake wakiltar yankin arewa a jihar Nasara, Sanata Philip Gyunka, ya bayyana rikicin jam'iyyar APC a matsayin babbar dama ce ga babbar jam'iyyar adawa PDP

Rikicin APC babbar dama ce ga jam'iyyar PDP - Sanata Gyunka
Rikicin APC babbar dama ce ga jam'iyyar PDP - Sanata Gyunka

Wani Sanata da yake wakiltar yankin arewa a jihar Nasara, Sanata Philip Gyunka, ya bayyana rikicin jam'iyyar APC a matsayin babbar dama ce ga babbar jam'iyyar adawa PDP. Da yake magana a karamar hukumar Arochukwu dake jihar Abia, a lokacin da jam'iyyar ta PDP take kaddamar da wani taro, Sanata Gyunka, wanda ya raka Sanata Mao Ohuabunwa zuwa wurin taron, yace jam'iyyar PDP jam'iyya ce da a yanzu duniya take kallo domin ta kawo canjin da jam'iyyar APC ta kasa kawowa al'umma.

DUBA WANNAN: Kwankwaso zai lashe kujerar shugaban kasa idan ya dawo NUP - Opara

Sanatan yace, "Idan nace canji ina nufin canji mai amfani, ba irin canjin da muke ciki ba a yanzu na bala'i da wahalar rayuwa, jam'iyyar APC mai mulki ta jefa cikin tashin hankalin da a tarihin kasar nan ba a taba shiga ba.

"Abinda yake faruwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari dama ce babba ga jam'iyyar mu ta PDP. Inda ace shugaba Buhari bai ci zabe ba da tuni yanzu ana ta cigaba da zagin mu. Allah ya kawo shine saboda ya tona asirin sa, akan bashi da wani abu da zai iya yiwa Najeriya," inji shi.

A lokacin da yake bayani ga al'ummar karamar hukumar Arochukwu, shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Cif Johnson Onuigbo, yace Najeriya tayi asarar duk abubuwan da ta samu kafin zuwan jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng