Ba duka aka zama daya ba: Kalli yadda wani Dansanda ke gabatar da Tafsirin Al-Qur’ani

Ba duka aka zama daya ba: Kalli yadda wani Dansanda ke gabatar da Tafsirin Al-Qur’ani

Watau ta tabbata a duk yadda al’umma sukakai ga lalacewa, ba a taba rasa mutanen kirki a tsakankaninsu, wannan yasa ba kasafai aka fiya yi ma mutane dukkaninsu kudin goro ba, walau na kirki ko na banza.

Wannan magana ta fi tabbata anan, inda kamar yadda yan Najeriya suka tambara Yansandan Najeriya a matsayin masu taya bera bari, yayin da wasu yan Najeriyan ke musu kallon maciya cin hanci da rashawa, sai ga shi an samu wani da ya karyata wannan tunanin na wasu yan Najeriya.

KU KARANTA: Cakwakiya: wata gada ta rufta da wani Gwamna da mataimakinsa yayin da suke daukar hoton ‘Selfie’

Ba duka aka zama da yaba: Kalli yadda wani Dansanda ke gabatar da Tafsirin Al-Qur’ani
DCP Ahmad

Legit.ng ta ruwaito an samu wani zakakurin jami’in Dansanda a garin Kaduna, mai mukamin mataimakin kwamishinan Yansanda, mai suna DCP Ahmad Abdulrahman, wanda ya fita zakka a hukumar Yansanda, inda yake baiwa jama’a ilimin addini.

Shi dai wannan jami’ain Dansanda yana gabatar da Tafsirin Al-Qur’ani ne a cikin wannan wata mai alfarma, watan Azumin Ramadana a babban Masallaci dake shelkwatar rundunar Yansandan jihar Kaduna.

Ba duka aka zama da yaba: Kalli yadda wani Dansanda ke gabatar da Tafsirin Al-Qur’ani
Tafsir

Ko a bara ma sai Sheikh DCP Ahmad Abdulrahman ya gabatar da Tafsiri, sai dai ya bayyana cewa marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ne ya basu kwarin gwiwar shiga aikin Yansanda don su kare mutuncin addinin Musulunci.

Ba duka aka zama da yaba: Kalli yadda wani Dansanda ke gabatar da Tafsirin Al-Qur’ani
Tafsir

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel