Tsohon Hadimin Kwankwaso zai yi takarar Gwamna da Ganduje

Tsohon Hadimin Kwankwaso zai yi takarar Gwamna da Ganduje

- Wani Matashi ya daura aniyar doke Ganduje daga kujerar sa

- Jafar Bello yace da shi za ayi takarar Gwamnan Kano a 2019

- Hadimin Kwankwaso zai yi takara ne a lemar Jam’iyyar PDP

Mun samu labari daga This Day a makon nan cewa wani daga cikin Hadiman tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso zai yi takara da Gwamnan Jihar na yanzu watau Dr. Abdullahi Umar Ganduje a zabe mai zuwa na 2019.

Tsohon Hadimin Kwankwaso zai yi takarar Gwamna da Ganduje
Jafar Sani Bello zai nemi kujerar Gwamnan Kano a 2019

Alhaji Jafar Sani Bello wanda ya taba aiki da tsohon Gwamna Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa zai nemi kujerar Gwamnan Jihar Kano a 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP. Jafar Bello yace lokaci yayi da Matashi zai fito takara a Jihar.

A jiya ne Alhaji Bello ya mika takardar sa ta shirin tsayawa takara a Jam’iyyar adawa na PDP. Matashin ‘Dan takarar yace dole a tashi tsaye domin ganin an babbako da harkar ilmi da kiwon lafiya da kuma noma a Jihar Kano tun da wuri.

KU KARANTA: Masu neman kujerar Gwamna Ganduje a 2019

Tsohon mai ba Kwankwaso shawara yace sama da shekara 30 kenan ana mulki a Jihar amma babu wanda yayi kokarin janyo masu hannun jari daga waje domin su zuba kudin su a Jihar. Bello yace sai dai sata kurum ‘yan siyasa su ka sa gaba.

Wani babba a Jam’iyyar PDP na Jihar Ibrahim Muhammad ya bayyana cewa Jafar Sani Bello Matashi ne da ya san aiki kuma tabbas zai iya yin gyara idan ya samu mulki. Ibrahim Muhammad yace PDP za ta tsaida ‘Dan takara na gari a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: