Wani matashi ya hau kolloluwar hasumiyar masallaci bayan ya yi zigidir
Wani matashi da ba a bayyana sunan sa ba ya haye kan kololuwar hasumiyar masallacin juma’a na unguwar Ja’en dake kan titin sharada a garin Kano.
Matashin ya yi zigidir haihuwar uwar sa bayan yah aye cikin hasumiyar. Ya tube kayan say a jefo su kasa.
Maidin masallacin, Mallam Adda’u, ya bayyana cewar matashin ya karya wata taga ne kafin ya samu dammar shiga masallaci kuma duk da sun yi kokarin dakatar da matashin hakan bata yiwu ba.
Sannan ya kara da cewa, matashin y ace ba zai sauko ba saboda wasu na neman shi zasu kasha shi, duk da bai bayyana ko su waye ba.
Wani daga cikin ‘yan kwamitin masallacin, Malam Kabiru, y ace sun sanar da jami’an ‘yan sanda bayan samun matashin cikin hasumiyar.
DUBA WANNAN: Babbar mota ta kashe mutane 10 a Zaria bayan ta kwace daga hannun direba
Daga bisani jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar sauko da matashin tare da tafiya das hi ofishin su domin zurfafa bincike a kan sa.
Kwanakin baya wani matashi ya taba haye kan kololuwar karfen gidan Radiyon Kano dake unguwar Tukuntawa tare da yin ikirarin cewar ba zai sauko ba sai an samar wa da matasa abin yi. Shi ma da kyar jami’an tsaro suka samu nasarar saukowa das hi daga karfen.
Bisa ga dukkan alamu matasan jihar Kano sun samo wani sabon salon hayewa kan gini ko karafa masu tsayi duk lokacin da suke da bukatar nuna fushi ko damuwar su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng