‘Yan fashi sun tare hanyar Abuja-Kaduna, sun kashe dan sanda da wasu mutane uku

‘Yan fashi sun tare hanyar Abuja-Kaduna, sun kashe dan sanda da wasu mutane uku

Da safiyar jiya ne wasu tsager da ake kyautata zaton ,yan fashi ne suka kasha wani dan sanda da direban wata motar haya yayin da suka tare babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

‘Yan bindigar sun datse hanyar ne a daidai Jere da misalin karfe 6:00 na safe tare da kwace kayan matafiyan da suka tare.

Dan sanda da aka harbe na daga cikin jami’an ‘yan sanda dake yaki da fashi da makami (SARS) dake aiki a kan babbar hanyar ta Abuja zuwa Kaduna.

‘Yan fashi sun tare hanyar Abuja-Kaduna, sun kashe dan sanda da wasu mutane uku
‘Yan fashi sun kashe dan sanda

Dan sandan ya mutu ne bayan harbin day a same shi yayin da suke musayar wuta da ‘yan fashin da suka tare hanyar.

Jaridar Premium Times ta frawaito cewar wani direba ya rasa ran sa bayan harsashi ya same shi bisa kuskure.

DUBA WANNAN: Ana fama da matsalar matsafa a Maiduguri, sun kashe wasu mata da kwakwule idon wani dattijo

An samu wani mummunan hatsari a kusa da inda ‘yan fashin da ‘yan sandan ke musayar wuta, mutane hudu sun mutu yayin da wasu 10 suka samu raunuka. Rahotanni basu tantance wane daga cikin abu biyu, fashi ko hatsarin, ya fara abkuwa ba.

An garzaya da gawar dan sandan da ta mutanen da suka yi hatsarin zuwa asibiti mafi kusa.

Kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Kaduna, Mukhtar Hussaini, yaa tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewar jami’an SARS din sun kai agaji ne bayan samun labarin abinda ke faruwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel