Wata mata ta kama mijin ta a filin jirgi suna shirin fita kasar waje da karuwar sa, leka kuji yadda ta kaya musu

Wata mata ta kama mijin ta a filin jirgi suna shirin fita kasar waje da karuwar sa, leka kuji yadda ta kaya musu

Wata mata ta kama mijinta da wata mata kiri-kiri a filin jirgi yayin da suke kokarin, hawa jirgi domin fita kasashen waje yawon shakatawa

Wata mata ta kama mijin ta a filin jirgi suna shirin fita kasar waje da karuwar sa, leka kuji yadda ta kaya musu
Wata mata ta kama mijin ta a filin jirgi suna shirin fita kasar waje da karuwar sa, leka kuji yadda ta kaya musu

Wata mata ta kama mijinta da wata mata kiri-kiri a filin jirgi yayin da suke kokarin, hawa jirgi domin fita kasashen waje yawon shakatawa. A cikin fushi, matar ta kama gashin daya matar yayin da ta kama su a filin jirgin saman, suna shirin shiga jirgin da niyyar fita wata kasar.

DUBA WANNAN: Sabuwar bullar Ebola a Afirka: Hukumar WHO ta fara gangamin shiri kar cutar ta balle

Matar ta kama su a babban filin jirgin sama na Jose Maria Cordoba dake birnin Rienegro, a arewacin kasar Columbia. Ta kama su a dai dai lokacin da suke shirin shiga jirgin domin zuwa wani wurin shakatawa a birnin Cartagena a yankin Carribean coast.

Wani wanda aka yi abun a gaban sa, wanda ya dauka da wayar hannu, mai suna Christos Kintis, ya dauki hoton bidiyon matar a lokacin da take rike da gashin dayar matar cikin fushi.

Ta ki yarda ta saki gashin matar wacce take cikin tashin hankali da radadin zafin rikon data yi mata, hakan ya tilasta mata kasa motsawa ko kadan, a can gefe kuwa mijin ne tare da wasu ma'aikatan filin jirgin suke ta kokarin baiwa matar tashi hakuri akan ta saki gashin dayar matar kada ta yi mata lahani.

An jiyo matar a cikin bidiyon tana korafin cewar mijin yayi mata alkawarin zai dauke su ya fita dasu yawo ita da dansu, amma kuma shine ya zagaye yazo zasu gudu shida ita.

A karshe mijin ya roki mutanen wurin dasu kira hukumar 'yan sanda domin kawo karshen lamarin, inda ita kuma matar take yi mishi ihun cewar karya yake yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel