Irin namijin kokarin da mu ke yi game da rikicin Birnin-Gwari – Buhari

Irin namijin kokarin da mu ke yi game da rikicin Birnin-Gwari – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa an kirkiro wata sabuwar bataliyar Sojoji a Yankin Birnin-Gwari domin kawo karshen rikicin Yankin da ya ki ci ya ki cinyewa na tsawon lokaci.

Mai magana da yawun bakin Shugaban kasar ya bayyana wannan a wani jawabi a Ranar Litinin. Hakan na zuwa ne bayan da Sarkin Garin ya bayyana cewa an kashe kusan mutane 60 a cikin kwanakin nan a wani hari da aka kai.

Irin namijin kokarin da mu ke yi game da rikicin Birnin-Gwari – Buhari
Jibril Zubairu Mai Gwari II ya koka da kashe-kashe

Shugaban kasar ta bakin Kakakin na sa yayi tir da kashe-kashen da ake yi a Yankin inda ya nemi a kafa karamar cibiyar Rundunar ‘Yan Sanda a karamar Hukumar. Shugaban kasar ya kuma kara Sojojin sama a Yankin na Birnin-Giwa.

KU KARANTA: Atiku Abubakar ya ba Gwamnatin Shugaba Buhari shawara kan sha'anin tsaro

A dalilin tabargazar da ake yi a Yankin, Gwamnatin Tarayya ta kara Sojoji a Yankunan Benuwe, Taraba, Zamfara, Nasarawa da ma Jihar Kaduna. Gwamnati ta kuma kafa cibiyar Sojojin sama a Taraba da kuma wata babbar Bataliya a Benuwe.

A jawabin Buhari yace bai ji dadin abin da ya faru a Yankin na Birnin-Gwari da sauran Jihohin kasa da ‘Yan ta’adda su ka tasa gaba ba. Idan ba ku manta ba kwanan nan Sojojin saman Najeriya su ka saye jirage domin kawo karshen matsalar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel