Miji ya kashe matar sa saboda bata dafa masa abinci ba ranar da take farincikin zagayowar ranar haihuwar ta

Miji ya kashe matar sa saboda bata dafa masa abinci ba ranar da take farincikin zagayowar ranar haihuwar ta

Wata mata, Sokari West, ta rasa ran ta sakamakon raunuka da ta samu daga yanka da kwalba da mijinta ya yi mata.

Rahotanni sun bayyana cewar, mijin da matar sun kaure da fada ne a gidan su dake Buguma a karamar hukumar Asari-Toru dake jihar Ribas saboda ta ki dafa masa abinci ranar da take farincikin zagayowar ranar haihuwar ta.

Jaridar Daily Sun ta rawaito cewar matar mai shekaru 33 sun fara samun matsala da mijin ta, Ibisaki, a kan batun rashin girka abinci a gidan su.

Miji ya kashe matar sa saboda bata dafa masa abinci ba ranar da take farincikin zagayowar ranar haihuwar ta
Miji ya kashe matar sa saboda bata dafa masa abinci ba ranar da take farincikin zagayowar ranar haihuwar ta

Majiyar jaridar Daily Sun ta shaida mata cewar, matar ta ki yin girki ranar Asabar tare da ficewar ta tare da kawaye domin bikin zagayowar ranar haihuwar ta.

Ma'auratan dama sun taba rabuwa saboda yawan fadan da suke yi kafin daga bisani su dawo su cigaba da zama tare.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun budewa 'yan jam'iyyar APC wuta a jihar Ribas

Majiyar ta ce mijin ya fasa kwalba tare da cakawa matar wurin tsinin, hakan ya jawo zubar jini da ya kai ga matar ta rasa ran ta bayan an garzaya da ita asibiti.

Bayan ya fuskanci matar ba zata rayu ba sakamakon yankan da ya yi mata, Ibisaki, ya mika kan sa ga ofishin hukumar 'yan sanda dake Buguma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel