Ma'aurata sun tona wa kansu asiri gaban kotu a jihar Oyo, leka kuji
- Wasu ma'aurata da ke zaune a garin Ibadan sun yiwa junansu tonon silili a gaban Alkali
- Mijin ya roki kotu ta raba aurensu saboda tsabar sata da yace matar nasa ke yi masa
- Matar nasa tace ita ba barauniya bane amma ta kwashe wasu kayansa ta sayar ne saboda ya dena kula da ita
Wata kotu da ke zamanta a Mapo da ke Ibadan a jihar Oyo ta raba auren wani Akeem Folorunsho da Fatima saboda sata da yayi ikirarin matar na yi masa. Ma'auratan dai sun shafe shekaru biyu suna tare kuma Allah ya albarci auren da 'da daya.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa Alkalin kotun Cif Ademola Odunade ya amince da bukatar Akeem inda ya raba auren.
KU KARANTA: Abin tausayi ya faru a Kano: Dalibi ya lume a ruwa garin ceton abokinsa
Akeem ya shaidawa kotu cewa matar nasa tana son ganin bayansa ne da halinta na sata. "Duk lokain da na fita daga gida don neman abinci, Fatima tana caje aljihun tufafi na kuma ta sace min kudi.
"Bayan abinci da kayan jaririn mu da na samar a gidan, ina bata N2,000 duk mako." inji shi.
Akeem kuma ya kara da cewa bayan ta bar gidansa, ta sake dawowa gidan inda ta balle kofan gidan kuma ta dauke masa kayayakin gida da suka hada da firinji, katifa, DVD player, kayan jin waka da sauransu.
A bangarenta, Fatima, wadda malaman makaranta ce ta musanta zargin daya ke mata na sata, ta fadawa kotun cewa mijin nata ya dena kulawa da ita ne duk da cewa bata gama murmurewa daga tiyata da akayi mata ba. Hakan yasa ta dauke wasu kayayakinsa ta sayar don ta biya wa kanta bukatu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng