Wani Barawo ya mika kansa ga Yansanda bayan buhun gyadan da ya sata ya makalkale masa a wuya (Hotuna)

Wani Barawo ya mika kansa ga Yansanda bayan buhun gyadan da ya sata ya makalkale masa a wuya (Hotuna)

Wani lamari mai ban dariya, man ban haushi, kuma mai ban tausayi ya faru da wani matashi da ya shahara wajen aikata sata, musamman yake bi cikin dare yana farautar kayan mutane, sai dai Hausawa na cewa idan ana cin kasa, a kiyayi na shuri.

Wannan matashin mai halin bera mai suna Frank Buhet ya takalo abinda yafi karfinsa, inda yaje ya sace ma wata tsohuwa buhun gyada da tsakar dare, amma koda yayi kokarin sauke buhun daga kansa a lokacin da ya isa gida, sai abu yaci tura, yayi yayi amma ina, buhu ya makale masa a wuya.

KU KARANTA: Kudi a kashe ta hanya mai kyau: Ronaldo ya baiwa budurwarsa kyautar Zoben naira miliyan 300 (Hoto)

Wani Barawo ya mika kansa ga Yansanda bayan buhun gyadan da ya sata ya makalkale masa a wuya (Hotuna)
Barawo

Wannan lamari mai ban al’ajabi ya faru ne a kasar Tanzania, matashin bayan ya fito daga gidan nasa ya dinga bi layi layi yana neman agaji a sauke masa gyadar amma an kasa, kai har kwanciya yayi a kasa ko buhun zai fado, amma abu yaci tura.

Legit.ng ta ruwaito bayan Buhet ya fahimci ya debo ruwan dafa kansa da wannan buhun da ya sato ne sai ya garzaya ofishin Yansanda, inda ya mika kansa da kansa, kuma ya bayyana musu yadda lamarin ya wakana.

Sai dai fa hatta a Ofishin Yansandan, buhun nan yaki sauka, kuma duk kokarin a Yansanda suka yi na kwantalo buhun daga kansa amma lamarin ya gagari kundila, don haka ne ya bayyana ma Yansandan gidan da yayi satar, kuma ya rokesu sun emo masa Tsohuwar don kada nauyi ya kashe shi.

Wani Barawo ya mika kansa ga Yansanda bayan buhun gyadan da ya sata ya makalkale masa a wuya (Hotuna)
Barawon

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng