Duniya tazo karshe: Za'a hana kiran Sallah a kasar Norway

Duniya tazo karshe: Za'a hana kiran Sallah a kasar Norway

- Wasu manyan jam'iyyu guda uku masu suna (Fremskrittspartiet-Frp) wadanda suka kafa gwamnatin hadin guiwa a kasar Norway sun bukaci a daina barin sautin muryan kiran Sallah yana fita zuwa wajen masallaci kasar

Duniya tazo karshe: Za'a hana kiran Sallah a kasar Norway
Duniya tazo karshe: Za'a hana kiran Sallah a kasar Norway

Wasu manyan jam'iyyu guda uku masu suna (Fremskrittspartiet-Frp) wadanda suka kafa gwamnatin hadin guiwa a kasar Norway sun bukaci a daina barin sautin muryan kiran Sallah yana fita zuwa wajen masallaci kasar.

DUBA WANNAN: Yayi niyyar komawa addinin musulunci matar shi ta hana shi

Shugaban kungiyoyin 'yan gudun hijira Jon Helgheim ya bayyanawa manema labarai cewar jam'iyyar tasu zata zauna ta tattauna a taron da zata yi na karshe a karshen wannan satin akan bukatar sun ta a dauki matakin da za'a hana sautin kiran Sallah da ake yi a cikin massalatai fita waje a fadin kasar.

Helgheim, ya kara da cewar bai san abinda kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya zata ce akan batun nasu ba, tunda kungiyar ta bayyana cewar hana kiran Sallah baki daya take hakkin dan adam ne, amma mu muna bukatar wadanda suke zama kusa da massalatai su dinga samun sukunin rayuwa ba tare da kiran sallar yana damun su ba.

A kasar Norway dai ana kiran sallah ne a cikin masallaci tare da yin amfani da lasifika domin wanda yake nesa ya san cewar lokacin sallah yayi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel