Ana wata ga wata: Gwamnatin jihar Kaduna ta maka El-Zakzaky a kotu bisa wasu caji takwas

Ana wata ga wata: Gwamnatin jihar Kaduna ta maka El-Zakzaky a kotu bisa wasu caji takwas

- Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da karar shugaban kungiyar 'yan uwa musulmi da aka fi sani da Shi'a

- Gwamnatin na tuhumar El-Zakzaky da wasu mutane uku da tayar da tarzoma da tunzura magoya bayan sa daukan makamai

- El-Zakzaky na tsare a ofishin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tun bayan kama shi a shekarar 2015

Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da karar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, shugaban kungiyar 'yan uwa musulmi da aka fi sani da Shi'a, a gaban kotun daukaka kara dake jihar.

An kama El-Zakzaky a watan Disamba na shekarar 2015 bayan wata arangama tsakanin magoya bayan sa da dakarun hukumar soji a Zaria.

Rahotanni sun bayyana cewar a kalla mutane 300 sun mutu yayin arangamar.

Ana wata ga wata: Gwamnatin jihar Kaduna ta maka El-Zakzaky a kotu bisa wasu caji takwas
Sheikh El-Zakzaky

Gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da El-Zakzaky gaban kotu bisa laifin hada baki domin tayar da husuma bayan kama shi a 2015.

Tun bayan kama shi, El-Zakzaky, na tsare a ofishin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) dake shelkwatar Abuja.

A wata sabuwar takardar kara da jaridar The Cable ta ce ta gani dake dauke da kwanan watan 18 ga watan Afrilu da muke ciki, gwamnatin jihar Kaduna ta sake maka El-Zakzaky da wasu mutane uku a kotun daukaka kara dake jihar bisa caji guda takwas. A takardar, gwamnatin jihar Kaduna ta ce zata gabatar da shaidu 18 a gaban kotu.

DUBA WANNAN: Yunkurin majalisar dattijai na tsige Buhari ya gamu da cikas

Ragowar mutanen da takardar karar ta ambata bayan sheikh El-Zakzaky su ne, Malama Zeenah Ibrahim, Yakub Yahaya Katsina da Sanusi Abdulkadir. Ana tuhumar su da ingiza mabiya Shi'a domin sabawa dokokin kasa tare da daure masu gindin mallakar miyagun makamai da suka hada da bindiga, adda, wukake, gatari, sanduna da sauran su.

Gwamnatin jihar ta ce tana ajiye da wasu makamai da aka kwace daga hannun mabiya Shi'a a matsayin shaida da zata gabatar gaban kotu.

A watan Janairu ne El-Zakzaky ya gana da manema labarai a karo na farko cikin shekaru biyu inda ya musanta jita-jitar cewar ya mutu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel