'Yan sanda sun kashe wani gawurtacen 'dan ta'ada a jihar Akwa Ibom

'Yan sanda sun kashe wani gawurtacen 'dan ta'ada a jihar Akwa Ibom

Hukumar Yan sanda na jihar Akwa Ibom ta bayar da sanarwan kashe wani gagararen shugaban kungiyar yan ta'adda, Isaac, wanda ya dade yana adabar mutanen kananan hukumomin Etim Ekpo da Ukanafun a jihar.

Hukumar ta Yan sanda ta nuna wa manema labarai da sauran mutane gawar shugaban kungiyar wanda akafi sani da Stainless a hedkwatan hukumar da ke Ikot Akpan Abia saboda hankalinsu ya kwanta.

'Yan sanda sun kashe wani gagararen shugaban kungiyar 'yan ta'ada daya adabi
'Yan sanda sun kashe wani gagararen shugaban kungiyar 'yan ta'ada daya adabi

Kwamishinan Yan sandan jihar, Adeyemi Ogunjemisi, yace rahotanni sun bayyana cewa dan ta'adan yana da hannu cikin laifuka da suka hada da kashe-kashe, fyade, garkuwa da mutane, da kona dukiyoyin mutane a garin karamar hukumar Etim Ekpo da Ukanafun.

KU KARANTA: 'Yan sanda sunyi caraf da wasu makiyaya dauke da miyagun makamai da kayan sojoji

Mr Ogunjemisi yace an kashe Isaac wanda akafi sani da Stainless ne a ranar 18 ga watan Afrilu a wata samame da hadin gwiwa tsakanin jami'an Yan sanda da wasu hukumomin tsaro. Sai dai bai fada a wurin da ake kashe shi ba.

Kwamishinan Yan sandan ya cigaba da cewa Isaac ya zama shugaban kungiyar yan ta'adan ne bayan jami'an tsaro sun kashe tsohon shugaban nasu mai suna Akaninyene Jumbo wanda akafi sani da Iso Akpafid.

Da wannan nasarorin da aka samu, hukumar Yan sandan tace an kawo karshen tashin hankali da fitina da Iso Akpafid da mukarabansa suka hadasa a kananan hukumomin Etim Ekpo da Ukanafun wanda sune biyu daga cikin kananan hukumomin da yan kungiyar asiri sukafi adaba a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164