Hodijan! Qabila dake sa yayyen amarya dandana Ango kafin su bashi diyarsu

Hodijan! Qabila dake sa yayyen amarya dandana Ango kafin su bashi diyarsu

- Wani yare a Uganda ya bada damar kanwar uwar amarya ta "dandana" Angon kafin aure

- Wani yare a kasar Uganda yazo da wani salon tantance ma mace miji wanda ya bambamta da sauran yarikan Afirika

- A al'adun Afirika da, kannin uwa an sansu da bada shawarwari ne da dabarun zama da miji kafin aure

Hodijan! Qabila dake sa yayyen amarya gwada karfin ango a gado kafin su bashi diyarsu
Hodijan! Qabila dake sa yayyen amarya gwada karfin ango a gado kafin su bashi diyarsu

Afirika dai nahiya ce mai girma, tana da albarkatun yarika da al'adu daban daban da suka hada da Zulu, xhoha, Himba, inyamurai, hausawa da kuma yarbawa. Nahiyar tana takama da kusan yarika dubu uku.

Su dai yaren Banyankole a kudu maso yammacin kasar Uganda dai abin ya bambamta. Idan masoya zasuyi aure, daya daga cikin amfanin kanwar uwa shine ta kwanta da Angon domin tantance jarumtarshi da kuma tabbatar da cewa zai iya haihuwa. Zata kuma duba amaryar domin tabbatar da budurcin ta kafin ayi auren.

A wasu al'adun ma Angon da amaryar zasu sadu a gaban kanwar uwar don tabbatar da komai na tafiya daidai.

Duk da dai zamuji wannan al'ada bambarakwai amma tana nuna mana yanda mutanen Banyankole suka dau budurci da muhimmanci.

Yarinya tana kai shekaru 8 da haihuwa ake sanya mata dokoki domin shirin auren ta.

A lokacin da tsararrakin ta a wasu al'adun suke wasanninsu na yarinta, yarinya dai a wannan al'adar tana kulle a gida inda za a dinga ciyar da ita nama, kunun dawa da madara har sai tayi kiba.

Yin kiba dai wata alamace ta kyau a yaren. Idan kuwa ta fara nono, iyayen ta zasu fada mata da ta guji duk abubuwan da zasu iya kai ga saduwa.

DUBA WANNAN: TAllafi don farfado da harkar manja

Hakkin uba ne ya samo wa Dan shi mata kuma ya biya dukiyar aure,wanda ya kunshi shanaye, akuyoyi da kuma tulun giya, iya dai karfin mutum.

Bayan an biya dukiyar auren sai shirye shirye su biyo baya. A ranar bikin ana shagulgula da dama inda uban amaryar zai yanka sa.

Gidan Angon ma ba a barinsu a baya domin kuwa a nan ake daura auren bayan kanwar uwar amaryar ta tabbatar da budurcin diyarta kuma ta "dandana" angon.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel