Zaben 2019: Ina rokon Allah kar ya ba Buhari ikon yin tazarce - Tsohuwar matar Obasanjo
Tshohuwar matar tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a wannan jamhuriyar Cif Olushegun Obasanjo mai suna Taiwo ta bayyana ra'ayin ta na cewa ko kusa ba ta fatan shugaban kasar Najeriya na yanzu ya sake tsayawa takara a 2019.
Uwar gida Taiwo din dai ta bayyana ra'ayin nata ne a yayin wata firar da ta yi da majiyar mu a karshen sati inda ta ayyana cewa ita yanzu tana ba shugaba Buhari shawara da ya tattara kayan sa ya koma jihar sa ta Katsina.
KU KARANTA: Ku sadu da Haijiya Zainab, tsohuwar matar Dangote
Legit.ng ta samu cewa haka zalika tsohuwar matar ta Obasanjo har ila yau ta kuma kara da cewa ita tana ma rokon Allah da kar ya ba shugaba Buhari damar zarcewar kamar dai yadda ya hana tsohon mijin ta yin tazarce karo na uku a shekarun baya.
A wani labarin kuma, Biyo bayan ayyana kudurin sake tsayawa takarar tazarce da shugaba Muhammadu Buhari yayi a satin da ya gabata yayin taron masu ruwa-da-tsaki na jam'iyyar APC mai mulki, alamu na ta nuna yiwuwar ficewar wasu jiga-jigan jam'iyyar zuwa wasu jam'iyyun domin samun tikitin takara a 2019.
Duk da dai har yanzu ba'a fallasa sunayen masu neman ficewa daga jam'iyyar ba, amma dai jam'iyyun da ake tunanin za su yi sabbin baki sun hada da Social Democratic Party (SDP), Labour Party (LP), Accord Party (AP) da kuma hadakar nan ta tsohon shugaba Obasanjo ta Coalition for Nigeria Movement (CNM).
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng