An kori jami'an diflomasiyyar Amurka 32 daga aiki bayan kama su da hotunan batsa a waya

An kori jami'an diflomasiyyar Amurka 32 daga aiki bayan kama su da hotunan batsa a waya

- A kasar Kambodiya ne ta'asar ta faru kan wasu jami'ai na Amurka

- Ana zargin suna lalata da karuwai ko ma wadanda shekarunsu basu kai ba a kasar

- Amurka na kokari wajen ganin ta gyara sunanta a idon duniya kan harkar banza

An kori jami'an diflomasiyyar Amurka 32 daga aiki bayan kama su da hotunan batsa a waya
An kori jami'an diflomasiyyar Amurka 32 daga aiki bayan kama su da hotunan batsa a waya

An kori ma'aikatan ofishin jakadanci 32 sakamakon zargin da ake musu na musayar hotuna da bidiyo na batsa.

Ofishin jakadanci Amurka da ke Cambodia ya kori mutane 32 bayan an kamasu suna musayar hotuna da bidiyo na batsa. Majiya daban daban Suka tabbatar da zancen ranar juma'a.

Majiya guda hudu ne suka ce bidiyon da hotunan batsa da suka kunshi yara yan kasa da shekaru 18 suke musaya a wata kungiyarsu a Facebook.

Matar daya daga cikin ma'aikatan taga hotuna da dama a inda ta kai karar ga shuwagabannin ofishin. A take aka tura zuwa ga ofishin bincike na tarayya "inji majiyar.

"An karbi katin shaidarsu kuma an duba wayoyinsu" tsohon ma'aikacin ofishin jakadancin wanda ya bukaci da a rufe sunanshi ya fada.

Yace a cikin ma'aikatan 32 akwai yan Cambodia da yan Amurka. Da yawansu masu gadi ne. Sunce babu mai wakiltar wata kasar a cikin su.

DUBA WANNAN: Dole Najeriya ta inganta kiwon lafiya daga kudaden ta

Korar tazo ne a lokacin tashin hankali tsakanin Cambodia da Amurka akan shugaba Hun Sen. Amurka dai sun musanta shiga siyasar Cambodia. Har yanzu dai Gwamnatin Cambodia bata ce komai ba akan wannan Korar.

Cambodia dai basa wasa da karuwancin yara duk da talauci da rashin zaman lafiya da aka sansu dashi. Sun daure mutane da dama wadanda ba yan'kasar ba akan hakan a shekarun da suka gabata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng