Allah yayi wa Sheikh Samaila Dakace rasuwa

Allah yayi wa Sheikh Samaila Dakace rasuwa

Wani babban malamin addinin musulunci a ke Kaduna, Sheikh Samail Abbas Dakace ya rasu yana da shekaru 64 a duniya.

Babban dan malamin, Abbas Samaila ne ya bayar da sanarwan rasuwar ga kamfanin dillanci labarai NAN a Zaria. Malamin ya rasu ne a jiya Alhamis bayan yayi fama da wata gajeuwar rashin lafiya.

Kafin rasuwar sa, an garzaya da malamin asibiti a garin Kaduna inda daga bisani ya rasu.

Malamin ya rasu ya bar matan aure guda hudu da yara 16.

Kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa babban Malami Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne ya jagoranci sallar jana'izar mamacin a kauyen Dakace da ke garin Zaria.

Allah yayi wa Sheikh Samaila Dakace rasuwa
Allah yayi wa Sheikh Samaila Dakace rasuwa

DUBA WANNAN: An kashe mutane 24 a wata sabuwar harin da makiyaya suka kai Binuwai - Majalisa

Marigayin malamin yayi karatun sa na addinin ne a garin Zaria daga baya kuma ya tafi kasar Masar, Senegal da Saudiyya don karo ilimi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: