Sauya jadawalin zabe: An bayyana sunayen ‘yan Majilasar Dattawa masu goyon bayan Buhari

Sauya jadawalin zabe: An bayyana sunayen ‘yan Majilasar Dattawa masu goyon bayan Buhari

An bayyana sunayen magoya bayan Buhari a Majalisar Dattawa game da batun canja jadawalin zaben 2019 a yayin da majalisar ke kokarin shafe bukatar shugaba Muhammadu Buhari a kan dokar zabe. Rashin cinma matsaya a gyaran dokar zaben, ya janyo rabuwar majalisar zuwa bangarori biyu.

Bangaren wasu daga cikin ‘yan majalisar suna goyon bayan bukatar shugaban kasa, wadda tsohon Gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu ke Jagoranta, sai kuma dayan bangaren wadanda basa goyon bayan shugaban kasar, su kuma shugaban majalisa ne yake jagoran su.

Sauya jadawalin zabe: An bayyana sunayen ‘yan Majilasar Dattawa masu goyon bayan Buhari

Sauya jadawalin zabe: An bayyana sunayen ‘yan Majilasar Dattawa masu goyon bayan Buhari

Kudirin dokar na shafe bukatar shugaban kasar ta tsallake zama na farko da akayi akanta, a ranar Talata. Wani daga cikin magoya bayan shugaba Buhari yace akwai ‘yan majalisa 42 da suka bayar da hadin kai game da biyawa shugaban kasa bukatarsa a kan doka.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari sune, Ali Ndume, Ahmed Lawan, Jibrin Barau, Ovie Oma-Agege, Abdullahi Adamu, Abu Ibrahim, da kuma Tayo Alasoadura.

KU KARANTA: Na shiga kungiyar asiri ne don cinma burina na zama dan siyasa

A wata takarda da aka gabatarwa jaridar Daily Trust bangarorin sun hada da Abia 0, Adamawa 3, Anambra 1, Akwa ibom 1, Bauchi 0, Binuwai 1, Bayelsa 0, Borno 1, Cross River 1, Delta 0, Ebonyi 1, Edo 1, Enugu 0, Ekiti 0, FCT 0, da Gombe 0.

Sashe na 58(5) na dokar kasa ta 1999 tace: “Inda shugaban kasa yake da wata bukata, kuma kudirin doka ya wuce a kowace majalisa ta wakilai da ta zartarwa, kuma an samu biyu bisa uku da suka goya baya, wannan kudiri ya zama doka, saboda ba za’ayi amfani da bukatar bukatar shugaban kasa ba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel