Muna son sanin adadin kudin da EFCC ta kwato da kuma inda suke ajiye - Ministar kudi

Muna son sanin adadin kudin da EFCC ta kwato da kuma inda suke ajiye - Ministar kudi

A yayin da ake samun mabanbantan alkaluma tsakanin manyan jami'an gwamnatin shugaba Buhari, Ministar kudi, uwargida Kemi Adeosun, ta aike da wasika zuwa ga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu, tana neman bayanai a kan adadin kudin da aka kwato da kuma inda aka ajiye su.

A watan Mayu na shekarar 2016, ministan yada labarai, Lai Mohammed, ya bayyanawa duniya cewar, gwamnati tayi nasarar kwato biliyan N78.3bn, Dalar Amurka miliyan $185m, Yuro miliyan £3.5m, da Fam €11,250.

Ya kara da cewar an karbo kadarori kimanin 239 da kuma wasu kudin da aka kwace na wucin gadi da adadinsu ya kai biliyan N126bn, Dalar Amurka biliyan $9bn, Yuro miliyan £2.4 da kuma Fam €303,399.

Muna son sanin adadin kudin da EFCC ta kwato da kuma inda suke ajiye - Ministar kudi
Muna son sanin adadin kudin da EFCC ta kwato da kuma inda suke ajiye - Ministar kudi

Sai dai alkaluman da Ministan ya bayar sun saba da na shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, kamar yadda ya bayyana a wajen wani taron kasa da kasa da a kan cin hanci da aka gudanar a birnin Vienna dake kasar Austria.

KU KARANTA: Da guda tilo wajen iyayensa ya sha guba bayan faduwa jarrabawar JAMB a karo na hudu

A cewar Magu, EFCC ta kwato kudi daga watan Mayu na shekarar 2015 zuwa watan Oktoba na shekarar 2017 da adadinsu ya kai biliyan N738.9bn kwatankwacin Dalar Amurka biliyan $2.9bn, tare da bayyana cewar "wadannan adadin bai shafi kananan kudade da muka karba irinsu Durham, CRA, da kudin nahiyar Turai."

"A cikin wannan shekarar kadai, EFCC ta kwato karin wasu kudaden da adadinsu ya kai biliyoyin Naira da Dalar Amurka.

Kudin sun hada da wadanda muka karbo daga hannun tsohuwar ministar man fetur, Diezani Madueke, da adadinsu ya kai Dalar Amurka miliyan $43m, da kuma wasu biliyan N2bn da aka sace daga hukumar 'yan sanda da kuma hukumar kula da birnin tarayya," a cewar Magu.

Wadannan mabanbantan alkaluma ne suka sanya Ministar ta kudi aikewa da Magu wata wasika tare da bukatar ya bayar da takamaiman adadin kudin da hukumar EFCC ta kwato da kuma inda kudin suke a ajiye.

Adeosun ta aike da wasikar ne ranar 9 ga watan Fabrairu, 2018, kuma ita da kanta ta saka hannu a kan wasikar. A cikin wasikar, Adeosun, ta ce tana bukatar Magu ya bayar da kididdigar adadin kudi da kadarorin da hukumar ta kwato, hade da takardun shaidar inda aka ajiye kudaden da kuma takardun shaidar kadarorin.

Majalisar dattijai ta ki tantance Magu ne saboda gazawar sa wajen bayar da takamaiman alkaluman kudin da hukumar ke ikirarin ta karbo.

Wani jami'in gwamnati dake aiki a ma'aikatar shari'a, ya ce, mai yiwuwa Magu na gwamutsa lissafin kadarori da kudaden da hukumar EFCC ta kwato.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng