Dandalin Kannywood: Yadda 'yan gulma suka so lalata aure na tun ina amarya - Mansura Isa

Dandalin Kannywood: Yadda 'yan gulma suka so lalata aure na tun ina amarya - Mansura Isa

Fitacciyar jarumar nan kuma tsohuwar fuska ta fina-finan Hausa a masana'antar shirya fina-finai da ake yiwa lakani da Kannywood watau Mansura Isa ta bayyana yadda aka so lalata mata aure tun tana amarya kimanin shekaru 15 da suka gabata.

Tsohuwar jarumar da ke zaman mata ga wani fitaccen jarumin kuma daya daga cikin ginshikai a masana'antar shirya fina-finan na Hausa da ma na turanci watau Sani Danja ta bayyana hakan ne yayin da ta yi wata fira da majiyar mu a kwanan baya.

Dandalin Kannywood: Yadda 'yan gulma suka so lalata aure na tun ina amarya - Mansura Isa
Dandalin Kannywood: Yadda 'yan gulma suka so lalata aure na tun ina amarya - Mansura Isa

KU KARANTA: Aina'u Ade ta ayyana lokacin auren ta

A cewar ta, ita ta godewa Allah da ya sa mijin ta yana da kyakkyawar fahimta ta rayuwa sannan kuma a koda yaushe yakan bata shawarwari tare kuma da kwarin gwuiwa akan dukkan lamurran da ta sa a gaba musamman ma dai na gidauniyar ta.

Haka zalika ta kara da cewa: "A farkon aurenmu mutane sun yi kiraye kiraye da turo masa tes, cewa wai, ba zama zan yi ba. Amma cikin ikon Allah, yau da gobe ta karyata su.

Hajiya Mansura ta ce yau ga shi bayan shan gwagwarmaya kala-kala da kuma kaikomo iri-iri na aurnen na su, yau gashi har yanzu suna tare sannan kuma kauna a tsakanin su sai ma dai abun da yayi gaba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng