Karfin hali barawo da sallama: Kotu ta yanke ma dalibin da yayi ma Sarkin Kano sojar gona

Karfin hali barawo da sallama: Kotu ta yanke ma dalibin da yayi ma Sarkin Kano sojar gona

Wani dalibi mai shekaru 20, Sultan Bello da ke yi ma Sarkin Kano sojan gona ya gamu da fushin wata kotun majistri dake zamanta a jihar Kano, inda ta bada umarnin garkame shi a gidan Kurkuku.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Alkalin Kotun Hassan Ahmad ne ya bada wannan umarni bayan sauraron laifuka guda uku da ake tuhumar Sultan, mazaunin Ja’oji, da suka hada da sojan gona, cin amana, da kuma bata suna.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Kaduna ya sanya tubalin gina gidaje 600 masu rangwame a jihar Kaduna

Da farin zaman na ranar Laraba 21 ga watan Maris, Dansanda mai shigar da kara Haziel Ledapwa ya bayyana ma Kotun cewar Sultan ya aikata laifukan ne a ranar 27 ga watan Feburairu ta wata shafin Instagram da yake amfani da shi da sunan mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II.

Karfin hali barawo da sallama: Kotu ta yanke ma dalibin da yayi ma Sarkin Kano sojar gona
San Kano

“Ya nemi kimanin kudi Naira miliyan 1.85 daga mutanen da suka hada da; Baraka Sani ta bashi naira miliyan 1.4, N150,000 daga Sadiq Saflan, N50,000 daga Sadiq Sani, N50,000 daga Aisha Ahmad, N50,000 daga Surajo Zakari da kuma N150,000 daga Yahaya.”

Dansanda ya kara da cewa Sultan ya nemi wadannan kudade ne da nufin biyan wata mawakiyar fina finan Hausa mai suna Zubaida Mu’azu da ta yi masa waka, a matsayinsa na Sarkin Kano, inda yace su tura kudaden zuwa asusun banki mai lamba 3049986447, bankin First Bank.

Daga karshe Dansandan yace hakan ya saba ma sashi na 132, 322 da 392 na kundin hukunta manyan laifuka. sai dai a zaman na ranar Laraba, Sultan ya amsa dukkanin laifukan da ake tuhumarsa, bayan nan kuma Alkali y adage sauraron karar zuwa 26 ga wata Maris.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng