Yan matan Dapchi 5 sun mutu sakamakon cinkoso, daya daga cikin yan matan da aka saki ta bayyana
Daya daga cikin yan matan Dapchin da Boko Haram suka saki a yau Talata ta ce kawayennsu 5 sun rasa rayukansu ne saboda cinkoso cikin motan da aka daurasu lokacin da akayi garkuwa da su.
Dalibar mai suna, Fatima Abdullahi, yar shekara 15 wacce itace mai lamba 73 a jerin yan matan da ma’aikatar yada labarai ta wallafa.
A hiran da tayi da wani Modu Geidam, wanda hadimin mahaifinta ne, Fatima ta ce an ajiyesu a ginin karkashin kasa ne saboda kada jiragen hukumar soji ya gansu.
An sako yan matan ne mako daya bayan shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyaran jaje makarantan da akayi garkuwa da yaran.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Boko Haram ta sako yan matan Dapchi, 5 sun rasu
Shugaba Buhari ya kai ziyara makarantan ranan Laraba, 14 ga watan Maris inda ya baiwa iyayen yaran tabbacin cewa gwamnatin tarayya ba zatayi kasa a guiwa wajen dawo da yaransu ba.
Dannan wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng