Rikicin Jam'iyyar APC ta Kaduna: Tsohon dan takarar Gwamna, Haruna Saeed ya fice daga jam’iyyar APC

Rikicin Jam'iyyar APC ta Kaduna: Tsohon dan takarar Gwamna, Haruna Saeed ya fice daga jam’iyyar APC

- Tsohon dan takarar Gwamnan jihar Kaduna ya fice daga jam'iyyar APC

- Na fice daga jam'iyyar APC ne saboda a mayar da shi saniyar ware a jam'iyyar inji Haruna Sae'ed Kajuru

‘Yan siyasa a jihar Kaudna sun gigice yayin da wani na kusa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kuma tsohon dan takaran gwamnan jihar Kaduna, Haruna Sa’eed Kajuru, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar APC.

Kajuru, wanda ya sanar da ficewar sa daga jam’yyar a APC a taron manema labaru a ranar Alhamis a birnin Kaduna, yace jam’iyyar bata ganin muhimmancin mutanen da suka kafa ta.

Haruna Sa’eed Kajuru, ya nemi gwamnan jihar Kaduna a shekara 2011 karkashin jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC) kafin ta zama jam’iyyar APC ta sanadiyar hadaka da wasu jam’iyyu.

Rikicin Jam'iyyar APC ta Kaduna: Tsohon dan takarar Gwamna, Haruna Saeed ya fice daga jam’iyyar APC
Rikicin Jam'iyyar APC ta Kaduna: Tsohon dan takarar Gwamna, Haruna Saeed ya fice daga jam’iyyar APC

Kajuru yayi ikrarin cewa shi ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna da aka gudanar a 2011 kafin jam’iyyar PDP dake kan mulki a lokacin ta murde zaben.

KU KARANTA : Kungiyar alkalai na kasa (NJC) ta bada umarnin korar alkalai biyu daga bakin aikin su

“Ina cikin jiga-jigan da suka kafa jam’iyyar APC dake mulki a jihar Kaduna da Najeriya baki daya, amma sai gashi yanzu an mayar da mu saniyar ware, ba a daukar mu da muhimmanci.

“Duk kokarin da muka yi na tabbatar da jam’iyyar APC ta samu nasara da karbuwa a jihar Kaudna ya zama shirme.

“Tunda naga bani da wani amfani a jam’iyyar kuma ba a gani na da muhimmanci ficewa daga jam’iyyar shine mafita a gare ne, “ inji Shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng