Dandalin Kannywood: Jarumi Adam A. Zango ya dawo Kano da zama

Dandalin Kannywood: Jarumi Adam A. Zango ya dawo Kano da zama

- arumi Adam A. Zango ya dawo Kano da zama

- Jarumin dan asalin karamar hukumar Zangon Kataf ne na jihar Kaduna

- A baya jarumin ya kwashe kayan sa gaba daya ya bar zaman garin na Kano

Fitaccen jarumin nan a shire-shiren fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood kuma mawaki Adam A. Zango, ya bayar da sanarwar cewa ya kammala shire-shiren sa na dawowa jihar Kano dake zaman tamkar cibiya ga harkokin fina-finan da zama.

Dandalin Kannywood: Jarumi Adam A. Zango ya dawo Kano da zama
Dandalin Kannywood: Jarumi Adam A. Zango ya dawo Kano da zama

KU KARANTA: Masana'antar Kannywppd tayi rashin jarumi

Jarumin wanda dan asalin karamar hukumar Zangon Kataf ne na jihar Kaduna har ila yau ya kuma sanar da hakan ne cikin wani sakon da ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumunta na Instagram.

Legit.ng dai ta samu cewa jarumin ya rubuta sako kamar haka a shafin na sa: "My Kano cribbbb!! The city need me that's why came back".

A baya dai mai karatu zai iya tuna cewa jarumin ya kwashe kayan sa gaba daya ya bar zaman garin na Kano biyo bayan wata 'yar rashin jituwa da ya samu da mutanen garin kan wata waka da ya yi ya kuma fitar mai taken 'Bahaushiya' da ta zama tamkar cin mutunci a garesu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel