Malaman addini sun ce yawun bakin mace yana da amfani

Malaman addini sun ce yawun bakin mace yana da amfani

- Sumbantar mace a baki yana da fa’ida matuka inji wani Shehin Malami

- Sheikh Guruntum yace miyau na Budurwa yana dada kaifin kwakwalwa

- Mai bukatar haddar sa ta zauna da kyau ya yawaita sumbantar iyalin sa

Wani Malamin addinin Musulunci ya bayyana cewa miyaun bakin mace yana da matukar amfani musamman ga masu kokarin hadda.

Malaman addini sun ce yawun bakin mace yana da amfani
Sheikh Guruntum yace yawun baki yana da amfani

Sheikh Ahmad Tijjanu Yusuf Guruntum wanda babban Shehin Malamin addinin Musuluni ne a Garin Bauchi a wani karatu da yayi ya bayyana cewa miyaun mace yana da amfani kwarai domin yana kara kaifin harda sosai.

KU KARANTA: Yadda wani Bawan Allah ya auri kanwar sa a Najeriya

A addinin Musulunci ma dai sumbantar iyali abu ne mai kyau inda wannan malamin ya bayyana wani babban fa’idar da ‘daliban ilmi ba su san shi ba. Malamin ya kafa hujja da wani hadisin Annabi a littafin Sahihul Bukhari.

Dama dai masana a kimiyya tuni sun ce sumbanta a baki yana taimakawa wajen maganin ciwon kai da rage ciwon hawan jini, haka kuma ana so mata masu al’ada su rika yawan sumbanta domin rage radadin al’adar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng