Rusa ginin APC: Gwamna El-Rufai yayi banza inji Shehu Sani

Rusa ginin APC: Gwamna El-Rufai yayi banza inji Shehu Sani

- Shehu Sani yace ko da an rushe masu Ofis amma akidar su na nan

- Sanatan yace ko harbe su Gwamnan yayi ba fa zai canza komai ba

- Sani yace wata rana Shugaba Buhari zai fahimci wanene El-Rufai

Sanatan Kaduna ta tsakiya watau Kwamared Shehu Sani yayi magana game da ofishin bangaren su na APC da aka rusa a makon nan. Shehu Sani yace wannan abin da Gwamnan yayi daidai yake da banza don babu abin da zai canza a gwagwarmayar su.

Rusa ginin APC: Gwamna El-Rufai yayi banza inji Shehu Sani

Shehu Sani yace nan gaba El-Rufai zai juyawa Buhari baya

Shehu Sani yayi magana da BBC Hausa a jiya yace su na nan a kan akidar su komin runtsi. Sanatan yace ya kamata Gwannan ya sani cewa mulkin zalunci da kama karya ba ya daurewa kuma da haka Damukaradiyya take da bai zama Gwamna ba.

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan wani Sanatan Jihar

Fitaccen Sanatan ya ja kunnen Shugaban kasa Buhari inda ya bayyana masa cewa sai bayan ya bar mulki zai fahimci wanene ainihin Nasir El-Rufai don a lokacin ne zai fito masa a mutum yayi ta sukar sa kamar yadda yayi wa irin su Obasanjo da 'Yaradua.

Kwamared Sani yace har wa yau su 'ya 'yan Jam'iyyar APC ne kuma su na tare da ita da ladabi don haka sun yi na'am da kwamitin sulhu da aka nada amma fa Sanatan yace su ba bayi bane kuma bai yiwuwa ace sai yadda Gwamna El-Rufai yake so za ayi a Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel