Amfani 8 na ruman ga lafiyar ɗan Adam
Shi dai itace ruman a turance ana kiran sa Pomegranate, kuma ya samo wannan suna ne daga sunan sa larabci wato Rumman, inda Allah madaukakin sarki ya ambace sa a wurare daban-daban a cikin ayoyin sa na Al-Qur'ani mai girma.
A sakamakon haka ne, wannan dan itace ya kasance daya daga cikin 'ya'yan itace masu matuƙar muhimmacin a duniya, domin kuwa Allah ya ambace shi a cikin aya guda tare da itacen zaitun, inda ya ƙunshi tarin sunadarai masu tasirin gaske ga lafiyar dan Adam.
Wannan dan itace ya ƙunshi sunadarai da suka hadar da; Fiber, Protein, vitamin C, vitamin K, Folate da kuma Potassium.
KARANTA KUMA: Kasuwancin da wasu jaruman hausa ke yi bayan shirin fim
Legit.ng ta kawo muku jerin cututtakan da dan itace ruman ke magancewa a sakamakon arzikin wannan sunadarai da ya ƙunsa:
1. Ciwon Zuciya.
2. Ciwon daji (musamman na mama, maraina da kuma mahaifa).
3. Rage teɓa da nauyin jiki.
4. Ciwon Sukari.
5. Hawan jini.
6. Cututtukan rashin ƙarfin mazakuta.
7. Kumburin jiki da ciwon gaɓɓai.
8. Cutar hauka da mantuwa.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kulla wata yarjejeniya da kasashen ketare biyar domin ciyar da Najeriya gaba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng